• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Ƴan sanda sun ƙwato yarinya ƴar shekara 12 da aka Daura wa aure da mai sheka 63

aksam by aksam
April 2, 2024
Reading Time: 1 min read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ƴan sanda sun ƙwato yarinya ƴar shekara 12 da aka Daura wa aure da mai sheka 63

Rundunar ƴan sandan ƙasar Ghana ta ce ta karɓo wata yarinya ƴar shekara goma sha biyu da ake zargi wani malamin cocin gargajiya mai ƙarfin faɗa-a-ji ya aura a ƙarshen makon jiya.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Wata sanarwar da rundunar ta fitar ranar Talata da asuba ta ce yarinyar, wadda ake zargi Gborbu Wulomo, Nuumo Borketey Laweh Tsuru XXXIII ya aura, tana hannunsu ita da mahaifiyarta.

“Rundunar ƴan sandan Ghana ta gano yarinyar ƴar shekara 12 da ake zargi an aurar da ita ga Gborbu Wulomo, mai shekara 63 a yankin Nungua na birnin Accra. Yanzu haka yarinyar da mahaifiyarta suna ƙarƙashin kulawar ƴan sanda,” in ji sanarwar.

Rundunar ta ƙara da cewa tana aiki da Ma’aikatar Kula da Iyali da Ƙananan Yara da Walwala ta Ghana domin bai wa yarinyar “taimakon da ya kamata” a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ƴan ƙasar Ghana, musamman masu mua’ala da shafukan sada zumunta, sun yi ta kakkausar suka bayan da wani bidiyo da ya nuna yadda ake ɗaura auren Gborbu Wulomo da yarinyar ƴar shekara 12.

A dokar ƙasar Ghana, ana aurar da mutum ne idan ya kai shekara 18.

Sai dai wata ƙungiya mai zamanta mai suna Girls Not Brides, ta ce ana aurar da kashi 19 na ƙananan yara mata a Ghana kafin su kai shekara 18 yayin da ake aurar da kashi 5 kafin su kai shekara 15.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wani Bishop ya caccaki gwamnatin tarayya kan Abu 2

Next Post

NDLEA ta kama ɗauri 20 na tabar wiwi da za a fitar zuwa kasar larabawa

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yanzu-yanzu yan bindiga sun  kashe mutane 9 tare da yin awon gaba da wasu da dama

Yanzu-yanzu yan bindiga sun kashe mutane 9 tare da yin awon gaba da wasu da dama

December 8, 2023
Yadda Alƙalin Wasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya Daga; Shugaban Wata Kungiyar Kwallon Kafa

Yadda Alƙalin Wasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya Daga; Shugaban Wata Kungiyar Kwallon Kafa

December 12, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media