• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yan Bindiga Sun Sace Basarake A Katsina

aksam by aksam
July 6, 2025
Reading Time: 3 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Daga Hassan Umar Gwammaja

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki a kauyen Karaɗuwa da ke ƙaramar hukumar Matazu a Jihar Katsina, inda suka sace wani basarake mai daraja a yankin

Wannan farmaki ya faru ne da safiyar ranar Juma’a,  5 ga watan Yuli, 2025 da misalin ƙarfe 3:30 na asuba, yayin da maharan suka isa kauyen dauke da muggan makamai a kan babura, inda suka kutsa kai cikin gidan Wakilin Hakimin Matazu a kauyen Karaɗuwa, Alhaji Abdullahi Muhammadu Bello, suka kuma yi awon gaba da shi.

’Yan Sanda Sun Kama Matasa 5 Da Ake Zargi Da Kwacen Waya A Adaidaita Sahu

Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa maharan sun harba bindiga a sama don tsoratar da mazauna yankin kafin su fice da basaraken zuwa daji.

Wani mai bibiyar lamurran tsaro a shafin X, wanda aka fi sani da Bakatsine, ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce:

“A daren jiya, ’yan bindiga sun sace Magajin Garin Karaɗuwa, Alhaji Abdullahi Bello. Karaɗuwa na ƙarƙashin ƙaramar hukumar Matazu ce a Jihar Katsina.”

Zuƙekiyar daukar matakin gaggawa daga jami’an tsaro bai kai ga ceto basaraken ba, sai dai rundunar ’yan sanda ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike tare da sintiri domin gano inda aka boye shi da kuma kamo masu laifi.

Rundunar ’Yan Sanda Ta Tarwatsa ’Yan Bindiga a Dutsinma, Ta Ceto Fursunoni

A wani harin daban da ya faru a cikin dare na ranar Juma’a, ’yan sanda a Jihar Katsina sun samu nasarar dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Dutsinma.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:45 na dare a unguwar Bayan Masallaci, kusa da Sabon Garin Safana, inda maharan suka yi garkuwa da wasu mazauna yankin.

Bayan samun kiran gaggawa daga mutanen yankin, DPO na Dutsinma ya hanzarta tura jami’ansa tare da motar yaki ta APC, inda suka ci karo da maharan a wajen garin Gidan Maifanfo, kuma aka yi musayar wuta mai zafi da su.

A cewar rahotanni, an samu nasarar ceto mutane biyu — Aminu Sani da Zainab Sani — daga hannun maharan, yayin da wani mutum mai suna Musa Sani ya samu harbin bindiga a kugunsa, wanda aka garzaya da shi zuwa Asibitin Gwamnati na Dutsinma domin samun kulawa.

Wata majiya daga rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto basaraken da aka sace a Karaɗuwa, tare da ɗaukar matakai na kara sa ido a kananan hukumomi da ke da rauni wajen fuskantar hare-hare.

Haka kuma, jami’an tsaro sun shawarci jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai da kuma gaggauta kai rahoto idan sun ga wani motsi da ba su amince da shi ba.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Ba Za Mu Bawa Kwankwaso Tikitin Takarar Shugabancin Kasa A Jam’iyyarmu— NNPP

Next Post

Yadda kotu ta yanke hukuncin shekaru 8654 ga wani Danjarida

aksam

aksam

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo
Uncategorized

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

by aksam
September 5, 2026
Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Il quadro attuale del mercato dei casinò online in Italia: innovazione, regolamentazione e prospettive future

April 23, 2025
Kotun Kolin Najeriya Taba Da Umarnin  A  Cigaba Da Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira Har Sai Baba Ta Gani

Kotun Kolin Najeriya Taba Da Umarnin A Cigaba Da Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira Har Sai Baba Ta Gani

November 29, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media