• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Ba Za Mu Bawa Kwankwaso Tikitin Takarar Shugabancin Kasa A Jam’iyyarmu— NNPP

aksam by aksam
July 5, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

Daga Hassan Umar Gwammaja

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana haka ne a hukumance cewa ba za ta sake bawa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, damar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar a babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Agbo Major, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 5 ga watan Yuli, 2025.

Yadda Cutar Amai da Gudawa Ta Kama  Dalibai 81 A Makarantar Gwamnati A Kaduna

Sanarwar ta zo ne a matsayin martani ga kalaman Alhaji Buba Galadima, wanda ya bayyana a kwanakin baya cewa Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa cikin NNPP kuma zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar.

Galadima ya ƙara da cewa babu wata alamar da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa jam’iyyar APC, kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, inda ya jaddada cewa “muna nan a NNPP kuma muna tare da Kwankwaso har 2027.”

Sai dai a cewar Dakta Agbo Major, “Kwankwaso da Galadima tuni an kore su daga jam’iyyar NNPP bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya da sabawa dokokinta.”

Ya ce, “Kwankwaso ba zai iya amfani da jam’iyyar NNPP don cimma wata manufa ta siyasa ba, domin kuwa tun bayan zaɓen 2023, jam’iyyar ta yanke duk wata alaƙa da Kwankwasiyya Movement.”

A cewarsa, jam’iyyar na ci gaba da ɗaukar matakan sake farfaɗo da martabarta da kuma tabbatar da daidaito a cikin gida, domin fuskantar babban zaɓen 2027 ba tare da rabuwar kai ba.

Jam’iyyar NNPP dai na daga cikin. jam’iyyun da suka fi ɗaukar hankalin jama’a a zaɓen 2023, musamman a jihar Kano, inda ta samu rinjaye mai faɗi. Sai dai rikicin cikin gida da ya biyo baya ya haifar da rabuwar kawuna tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, wanda ya kai ga kore Kwankwaso da wasu daga cikin masu biyayya gare

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, Ya Karɓi Gaisuwa Daga Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau

Next Post

Yan Bindiga Sun Sace Basarake A Katsina

aksam

aksam

RelatedPosts

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa
Uncategorized

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

by aksam
June 15, 2026
Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato
Uncategorized

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

by aksam
June 2, 2026
Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa
Uncategorized

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

by aksam
May 31, 2026
Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya
Uncategorized

Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya

by aksam
May 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Musa Garba Kwankwaso (BABA), Ya Ce Zai Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawar Kasannan

Ya Kamata Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Tsare Mutuncinta;- A Cewar Wasu Al’umma

April 6, 2025
Sakacin Jami’an Tsaro Ne Ya Sa Masu Zanga-Zanga Su Ka Yi Barna A Jihar Kano:–  Sarkin Kano Na Goma 16 Muhammadu Sunusi ll

Zargin Karya Dokar Hawan Sallah: Rundunar ‘Yansanda Ta Kasa Ta Aikewa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na II Takardar Sammace

April 5, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media