A baya mutane da dama na kallon makamin Fattah a matsayin gama-garin makami, Ashe lamarin yafi karfin Binciken Turawan yammacin duniya.
1:Babban abin mamaki a jikin wannan makami shine : yana dauke da Na’urar dusashe na’urar kariya ta Irone Dome na Amurka wanda Isra’ila ke amfani da shi.
2: Fattah makami ne na ballistic missile mai saurin gaske (hypersonic missile) wanda Iran ta kera da kanta. Yana da ikon wuce sauti har sau ba adadi (hypersonic speed), wanda hakan ke sanya shi da wuya a cafke ko a kare kai daga gare shi.
3: Yana tafiya da sauri fiye da Mach 13 (fiye da sau 13 na saurin sauti), wanda ya fi yawan makaman kariya na ƙasashe da dama.
4: Makamin na da ikon kaucewa na’urorin kariya da garkuwa (missile defense systems), saboda yana iya sauya hanya cikin sauri yayin tashi.
5: Fattah na da ikon kai harin daga nisan fiye da 1,400 kilomita, wanda hakan ke bashi damar kai hari ga wurare da dama a yankin da ke makwabtaka da Iran.












