• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Wani gwamna ya goyibayan karar da SERAP ta shigar da gwamnoni 36

aksam by aksam
May 8, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
470
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ƙungiyar kare ‘yancin ‘yan ƙasa da Bibiyar Ayyukan gwamnati ta SERAP ta maka Gwamnonin jihohin 36 na Najeriya da Ministan Abuja babbar kotu a jihar Legas bisa zarginsu da gazawa wajen ƙididdigar ayyukan da suka yi da kudaden lamuni da suka karba da ya kai har dalar Amurka biliyan 4.6 da kuma Naira tiriliyan 5.9.

A karar da ta shigar, SERAP na son kotu ta ba wa Gwamnonin umarnin gayyato hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC, domin su binciki yadda Gwamnoni da Ministan Abuja suka salwantar da kuɗaɗen lamunin da aka ba su.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Kazalika, SERAP ta ce, doka ta ba wa ‘yan Najeriya ‘ƴancin sanin yadda Gwamnoni suka salwantar da kuɗaɗen lamunin da suka ƙarba, tunda da sunansu aka ba su rancen.

Kungiyar dai ta ce a rahoton da ta tattara, na cewa gwamnonin na karkatar da akalar kuɗaɗen lamunin, da kuma wadaƙa da su wajen biyan buƙatunsu.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi A. Sule, ya ce “manufofin bin diddigin ayyuka da kungiyar SERAP ke yi abu ne mai kyau, sai dai kungiyar na aiwatar da ayyukanta ne, ba bisa yadda ya dace ba, domin kamata ya yi ace kungiyar ta samu masu ilimin da za su gudanar da ire-iren wadannan bincike, ba tare da siyasantar da lamuran ba.

Gwamna Sule, ya ce idan har wannan bin diddigin ayyuka da kungiyar ke yi, domin bata ma wani suna ne, to ba za su samu hadin kan jama’a ba”.

Barrister Haruna Magashi, lauya mai zaman kansa, kuma ya ce “sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasa, ya ba wa shugaban kasa, da mataimakinsa dama gwamnoni da mataimakansu, kariya akan cewa baza’a iya shigar dasu kara kotu ba, idan har suna kan karagar mulki.

Barrister Magashi, ya kara da cewa amma “wannan tanadi na kariya da kundin tsarin mulki ya basu, ba zai hana a shigar da ofisoshinsu kara ba”.

A hirarsa da Muryar Amurka, Dr. Isa Abdullahi Kashere manazarci kuma masanin tattalin arziki a Jami’ar Tarayya dake Kashere Jihar Gombe ya ce “dole kungiyar SERAP ta yi zargin Gwamnoni sun yi wadaƙa da kuɗaɗen lamunin da aka ba su, ganin cewa ansha basu ire-iren wannan kuɗaɗe amma talaka baya gani a ƙasa.

Kungiyar SERAP dai na buƙatar gwamnoni da ministan babban birnin tarayya Abuja, da su gabatar da yadda suke salwantar da biliyoyin kuɗaɗen da ake ba su, domin ta haka ne za a iya magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma kauce wa zargi

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Shugaban Najeriyan ya Isa fadarsa bayan shafe kwanaki a kasashen ketare

Next Post

Majalisar wakilai ta umarci CBN ya dakatar da shirinsu na daukar 0.5

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

‎Kotun Soji A Najeriya Ta Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

‎Kotun Soji A Najeriya Ta Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

April 29, 2025
Jami’an Tsaron DSS Sun Kama Wani Mutum Da Kuɗi Naira Miliyan 25 Dake Zargin Na Sayen Kuri’one A Zaben Cike Gurbi

Jami’an Tsaron DSS Sun Kama Wani Mutum Da Kuɗi Naira Miliyan 25 Dake Zargin Na Sayen Kuri’one A Zaben Cike Gurbi

August 16, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media