Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna.
A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci.
Jaridar Daily truth ta rawaito cewa a wata sanarwa da kakaki rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabi’u Muhammad, ya yaba wa haɗin gwiwar jami’an tsaro, inda ya bayyana kama mutumin a matsayin wani muhimmin mataki na kare martabar zabe.
Aksam Media ta gano cewa CP Rabi:u ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana ƙoƙarin kawo cikas ga zaben, zai fuskanci hukunci ba tare da la’akari kuwaye ba.












