DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya Amince Da Yin Murabus Na Dagacin Garin Takai a Yankin Karamar Hukumar Dawakin Kudu Malam Ummaru Mamudu, Sakamakon Tsufa Da yi, tare da Nada Dansa a Matsayin Wanda zai Gajeshi a Yayin Zaman Fadar Na Yau Litinin.
Sarkin Na Gaya Ya tambayi Al-umar Garin Na Takai cewa sun Amince Da Yin Murabus din Na Dagacin nasu,suka amsa cewa sun amince,nan take Sarkin ya bada umarnin Aje a Nada Dansa Malam Nuhu Ummaru Matsayin Sabon Dagacin Garin .
Da Yake Jawabi Tun Da Farko,tsohon dagacin Gundumar ta Takai a Karamar Hukumar Dawakin Kudu Malam Umaru Mamudu Ya Ce a shafe Kusan Shekaru Hamshin yana Jagorancin Alumar Gundumar Takai,ga Kuma Tsufa ,hadi Da Rashin Lafiya Da Yake fama da ita yasa ya Yanke Shawarar yin Murabus ya bawa Dansa Nuhu Ummaru Mamudu.
Anasa Bangaren Hakiman Dawakin Kudu Turakin Gaya Alhaji Ja’afar Usman Muhammad ya baiyana Cewa Dagacin Garin Takai Na Daga Cikin Tsoffin Dagatai a Gundumar Dawakin Kudu,ya qara Kira Ga Alumar Garin Takai da Su ci Gaba Da Bawa Malam Nuhu Ummaru Hadin Kan Da Ya Kamata dan gudanar da Ayyukansa Cikin Nasara.
Jami’in Yada Labarai Na Masarautar Gaya Auwalu Musa Yola ya rawaito cewa Sabon Dagacin Garin Na Takai Malam Nuhu Ummaru Mamudu ya baiyana farin cikinsa , sakamakon Gadar Mahaifin sa da yi ,tare da rokon Alumar Garin Na Takai da Su bashi Hadin Kan Da Goyon Bayan da ya dace a Wajen gudanar da Ayyukansa.










