Daga Hassan Umar Gwammaja
Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa ƴan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, sun kashe shi.
A cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya ‘yan bindigar kudin fansa da suka bukata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.
Mako uku da suka wuce ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da sarkin a yankin kwanar maharba lokacin da yake kan hanya bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.
A hirarsa da BBC Hausa, Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne magajin garin Gobir, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a jiya Talata.
“Labarin da na samu shi ne ‘yan bindigar sun harbe shi ne tun a jiya [Talata] bayan la’asar, kuma waɗanda suka je tattauna biyan kuɗin fansa ne suka ga gawar sarkin a kwance,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da aka yi magana da shi ba su samu gawar mai martaban ba tukunna..










