Hukumar yaki da rashawa ta Kano (PCACC) ta cafke dan uwan Sanata Rabiu Kwankwaso da wasu mutane hudu kan zargin rashawa
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin an karkatar da kimanin Naira biliyan 10 a kwangilar sayo magunguna
Binciken farko na hukumar ne ya ba ta kwarin guiwar kamo Musa Garba Kwankwaso, shugaban karamar hukuma da wasu uku
Arise TV ta ruwaito cewa PCACC ta cafke mutane biyar da suka hada da dan uwan Kwankwaso, da kuma babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi, Mohammed Kabawa.
Sauran da aka kama sun hada da shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON na jihar, Abdullahi Vashir wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Tarauni.
Hakazalika, hukumar yaki da rashawar ta cafke shugaban kamfanin magunguna na Novomed, Musa Kwankwaso, dan uwa ga jagoran NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso.
Dalilin kama dan uwan Kwankwaso An zargi wadanda aka kama da hada baki wajen bai wa Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomin jihar ba tare da bin dokar ba da kwangila ba.
Binciken farko ya nuna cewa kowacce daga cikin kananan hukumomin 38 sun biya Novomed N9.150m domin siyan magunguna amma har yanzu ba a kawo musu magunguna ba










