• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Trump ke fuskantar caccaka daga Lauyoyi a Amurka bayan korar shugabar hukumar lafiya ta ƙasar

aksam by aksam
August 28, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Fadar gwamnatin Amurka – White House ta ce ta kori shugabar hukumar yaki da cutuka ta kasar Susan Monarez bayan da ta ki yarda ta ajiye aikinta a ranar Laraba.

A wata sanarwa ta fadar ta ce tsarin Dr Monarez ya saba da manufar Shugaba Donald Trump, saboda haka an cire ta daga shugabancin hukumar ta lafiya.

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Tun da farko ma’aikatar lafiya ta Amurka ce ta sanar da saukar darektar, wanda hakan ya sa lauyoyin Dr Monarez suka fitar da sanarwa da a ciki suka ce ba a gaya mata sallamar tata ba kuma ba za ta sauka daga aikin ba.

Lauyoyin sun ce gwamnati ta dora mata karan-tsana ne saboda ta ki yarda ta zama rakumi da akala kan manufofi da umarnin gwamnati marassa kan gado da za su iya jefa lafiyar al’umma cikin hadari, tare kuma da zargin sakataren harkokin lafiya na Amurkan Robert F Kennedy Jr da amfani da harkokin lafiyar al’umma a matsayin makami.

Bayan wannan wasika ta lauyoyin nata ne sai kuma fadar gwamnatin Amurka ta fitar da wata sanarwa wadda a ciki take cewa – kamar yadda lauyoyin Susan Monarez suka tabbatar – a wasikarsu matar ta yi hannun riga da manufofi da tsare-tsaren Trump, a don haka an cire ta daga mukamin darektar hukumar yaki da cutaka ta Amurka, (CDC).

Shugaba Trump ne ya zabi Dr Monarez wadda ta dade a matsayin masaniyar kimiyya ta gwamnatin Amurka – ta shugabanci hukumar hana bazuwar cutukan – kuma a watan Yuli ne majalisar dattawan kasar ta amince da ita.

Trump ya zabe ta ne a wannan mukami bayan da ya janye sunan mutumin da ya fara zaba da zai shugabanci hukumar – tsohon dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican, Dave Weldon – wanda aka soke shi a kan ra’ayinsa game da riga-kafi da kuma cutar galhanga.

Sanarwar barin Dr Monarez wannan shugabanci na hukumar – da ma’aikatar lafiya ta Amurka ta yi ke da wuya sai wasu manyan shugabannin hukumar akalla su uku su ma suka sanar da saukarsu daga mukamansu na hukumar.

Saukar manyan jami’an da ta zo tamkar watsewar ‘ya’yan zabi – ta kasance ne kan yadda kwararru a harkar lafiya ke nuna damuwa a kan yadda hukumar ke daukar harkar rigakafi a karkashin jagorancin sakataren harkokin lafiya na Amurka Kennedy – wanda mutum ne da ke nuna shakku da tababa a kan allurar rigakafi.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Dakile matsalar tsaro: Kungiyar yan kasuwar Rimi ta fito da sabbin dabarun koya sana’o’i ga matasa

Next Post

Kungiyar Direbobi ta Jihar Kano reshen kofar Wambai ta aika muhimmin sako ga Gwamnatin Kano

aksam

aksam

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala
LABARAI

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

by aksam
April 17, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID
Uncategorized

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

by aksam
April 17, 2026
Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka
Uncategorized

Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka

by aksam
April 11, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

The Most Rewarding Slot Machines at lbspins casino

April 21, 2025
Bayan kai hari garin Kahutu Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Bayan kai hari garin Kahutu Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

June 28, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media