Yakara da cewa Ta’addanci da rashin tausayin da ‘yan ta’ada suka aikata akan sa, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar gawurtaccen basaraken babbar barazana ce akan ɓukatar da ake da akwai na inganta tsaron ƙasar nan don kare lafiya da dukiyoyin al’uma
wajen nuna damuwa da ɗaukar matakin daya kamata akan lokaci ya taimaka wajen samun kai a cikin wannan hali na ni ‘ya su
Yana da kyau mu sake jaddadawa anan cewa ya zama dole gwamnati ta samar tsaro da zai tabbatar da bada kariyar rayuka da kuma dukiyoyin al’uma, ta hanyar da ‘yan ƙasa ba za su cigaba da zaman ‘ɗar ‘ɗar dangane da faɗawa tarkon ‘yan ta’adda ba.
A karshe yayi adduar Allah ya karbi shahadar sa ya kuma ba iyalan da yan uwa hakurin wannan babban rashi











