Daraktan Harkokin Musamman na Ma’aikatar, Sani Abba Yola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Taron ya tattaro tsofaffin ‘yan jarida, masu aikin jarida na yanzu, malamai a fannin, shugabannin ƙungiyoyi, shugabannin gidajen jarida, manyan edita, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa aikin da bin ƙa’ida da kuma sake fasalta aikin jarida a Kano da ma kasa baki ɗaya.
Wannan zama, wanda ya kasance wani bangare na taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na NUJ na tsawon kwanaki biyu, ya bayar da damar musamman ga gogaggun ‘yan jarida su raba ƙwarewarsu ga matasa, tare da tattauna ƙalubalen zamani da ke fuskantar aikin aikin
A jawabinsa, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya tabbatar da aniyar gwamnatin Kano na samar da yanayi mai sauƙi ga ‘yan jarida.
Ya yaba wa NUJ bisa zaɓar Kano wajen gudanar da taron NEC, tare da alkawarin ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen ƙungiyar na inganta yada sahihan bayanai ga jama’a.
Comrade Waiya ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da biyan basussukan fansho na tsofaffin ‘yan jarida, saka jari a harkar kafafen yada labarai, inganta horar da ma’aikata, da kuma ɗaukar matakan shawo kan matsalolin tsaro a jihar.
Shima shugaban NUJ,na kasa Comrade Alhassan Yahaya, ya bayyana taron a matsayin girmamawa ga tsofaffin ‘yan jarida bisa gudunmawar da suka bayar ga al’umma, yana mai kiran su “ido na jama’a”.
Ya yi tsokaci kan dokar Media Enhancement Bill, wacce ke neman inganta walwalar ‘yan jarida ta hanyar tanadin inshora da sauran kariya, domin ƙarfafa yin rahotanni na gaskiya da ɗabi’a.
Tsohon shugaban NUJ na ƙasa, Comrade Sani Zoro, ya tuna irin rawar da ƙungiyar NUJ ta Kano ta taka a matakin ƙasa, da yawan fitattun shugabanni da ta bayar.
Tsofaffin jami’an gwamnati da masana da suka yi jawabi sun haɗa da Alhaji Baba Halilu Dantiye, Farfesa Umar Faruk Ibrahim, Alhaji Muhammad Danyaro, Alhaji Ahmed Aminu, Farfesa Sule Ya’u Sule, da Alhaji Abdulkadir Ahmad Kwakwatawa.
Sun shawarci matasa ‘yan jarida da su kiyaye ƙa’idar aiki domin samun ingantacciyar makoma, tare da bayar da shawarwari kamar:
Yin taron tattaunawa a kai a kai domin ci gaba da ɗaukaka ƙa’idoji.
Tsofaffin ‘yan jarida su rika ba matasa shawarwari ta hanyar dandamali na zamani.
Samar da wuraren haɗuwa ga tsofaffin ‘yan jarida domin musayar ilimi.
Tabbatar da cewa tashoshin watsa shirye-shirye suna ɗaukar ma’aikata masu ƙwarewa.
Kafa tsarin yabo da kyauta ga masu bin ka’ida.
Fitar da shirye-shiryen da suka dace da al’adun jihar.
Taimaka wajen kafa tashoshin talabijin masu zaman kansu don ƙara farin jinin Kano a matakin ƙasa.
Taron ya kuma amince da ƙirƙirar Kungiyar Tsofaffin ‘Yan Jarida ta Kano, wacce za ta rika bayar da shawara da horo tare da kiyaye tarihin da ingancin aikin jarida a jihar.
An kafa kwamiti mai mutane tara domin tsara tsarin aiki da ƙa’idojin shiga kungiyar. Membobin sun haɗa da:
Alhaji Baba Halilu Dantiye
Alhaji Ahmed Aminu
Alhaji Mohammed Danyaro
Alhaji Abdulkadir Kwakwatawa
Farfesa Umar Faruk Jibril
Farfesa Mai Taimako Sule Ya’u Sule
Dakta Saminu Umar Rijiyar Zaki
Mustapha Gambo Muhammed
Hauwa Sulaiman Zaharaddeen.












