• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Ƴan Najeriya Sama da Miliyan 1.9 Ne Su Ka Nemi Aikin Immigration da Fire Service A Ƙasa da Wata Ɗaya

aksam by aksam
August 11, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

Daga Hassan Umar Gwammaja
Allah ’yan Najeriya 1,911,141 ne suka nemi shiga aikin Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) kafin rufewar shafin neman aiki a ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, kamar yadda PUNCH Online ta gano.

An samu matsalolin fasaha a daukar ma’aikatan na shekarar 2025, inda shafin ya rika katsewa, dalilin hakan ya sa aka dakatar da shi na wani lokaci.

An fara shirya fara wannan daukar aiki tun ranar 26 ga Yuni, amma daga baya aka dage zuwa 14 ga Yuli, sannan aka sake daga shi zuwa 21 ga Yuli.

Saboda haka, lokacin da aka tsara rufe shafin shi ne ranar 4 ga Agusta, 2025,amma sai aka kara mako guda zuwa Litinin, 11 ga Agusta.

Duk da wadannan matsaloli, alkaluman da ke shafin CDCFIB sun nuna cewa mutane 1,911,141 ne suka nemi aikin kafin rufe shafin.

A cewar alkaluman, jihohin da suka fi yawan masu nema sun hada da Kogi (116,162), Kaduna (114,536), da Benue (110,565), yayin da Bayelsa (11,669) da Lagos (14,216) suka fi karanci.

Jihohi biyar da suka fi yawan masu nema su ne Kogi, Kaduna, Benue, Kano, da Niger, wadanda suka samar da jimillar masu nema 510,174.

A bangaren wadanda suka fi karanci kuwa, Bayelsa (11,669), Lagos (14,216), Rivers (22,210), Ebonyi (23,601), da Delta (27,962) sun hada gaba daya da masu nema 99,658.

A halin yanzu, CDCFIB ta bayyana matakan da masu nema za su bi bayan kammala neman aiki na shekarar 2025 ga hukumar tsaro ta paramilitary.

A cikin wasu sakonni da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, hukumar ta gode wa masu nema tare da bayyana cewa za a tuntubi wadanda aka zaba cikin ’yan kwanaki masu zuwa, tare da umarni kan mataki na gaba.

Hukumar ta shawarci masu nema da su rika duba sakonnin imel da na waya akai-akai, tare da shiga shafin CDCFIB da kafafen sada zumunta don samun sabbin bayanai.

Ta ce: “An rufe shafin neman aiki ! An rufe shafin neman aiki na Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board. Muna gode wa duk masu nema bisa sha’awar su da jajircewa wajen yi wa kasa hidima cikin kima, gaskiya, da alfahari.

“Mataki na gaba! Za a tuntubi wadanda aka zaba cikin ’yan kwanaki masu zuwa tare da karin bayani. Don Allah ku rika duba imel da sakonnin waya, kuma ku kasance kuna binciken shafin da kuma kafafen sada zumunta don samun muhimman bayanai.”

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnan Kano Ya Buƙaci Kwamishinan Ma’aikatar Jinƙai Da Rage Raɗaɗin Talauci Da Ya Kula Da Ma’aikatar Sufuri Na Wucin Gadi.

Next Post

NUJ da Gwamnatin Kano Sun Kafa Kungiyar Tsofaffin ‘Yan Jarida, a jihar Kano domin kara wayarwa da kananan ‘yan jarida kai dangane da aikinsu

aksam

aksam

RelatedPosts

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026
Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito
Uncategorized

Gwajin DNA: Kashi 23.6% Na Gwaje-Gwajen Uba A Najeriya Sun Nuna Rashin Daidaito

by aksam
August 25, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Sule Lamido ya soki hadakar jam’iyar ADC  ya Jadda zaman sa a PDP

Sule Lamido ya soki hadakar jam’iyar ADC ya Jadda zaman sa a PDP

July 23, 2025
Muhammad Sanusi ll ya yi tsokaci kan matsalolin suka dabaybaye Najeriya

Muhammad Sanusi ll ya yi tsokaci kan matsalolin suka dabaybaye Najeriya

July 4, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media