• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kwace jiragen shugaba Tinibu, gwamnatin tarayya ta magantu

aksam by aksam
August 16, 2024
Reading Time: 3 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

A ranar Alhamis ne labarin hukuncin wata kotun Faransa ya bazu a Najeriya, wadda ta zartar da hukuncin miƙa wasu jiragen Shugaban Najeriya ga wani kamfani na ƙasar Sin.

Tun da farko kamfanin ya buƙaci kotun ne ta ba shi damar ƙwace wasu kadarorin gwamnatin Najeriya da darajarsu ta kai ta kuɗi fam miliyan 74.5 da ke ƙasashe takwas na duniya.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Company Limited ne ya nemi buƙatar hakan domin samun diyya kan wata rigimar kwantila da ta shiga tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.

A nata ɓangare gwamnatin Najeriya ta zargi kamfanin na ƙasar China da yaudarar kotun don cimma wani muradin ko son ranta.

Cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai taimaka wa Shugaban kasa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai ya fitar ranar Alhamis, ya yi zargin cewa kamfanin na yunƙurin amfani da yaudara don ƙwace wa ƙasar kadarorinta.

Ya ƙara da cewa kamfanin Zhongshan, “ba shi da gamsassun hujjojin da zai buƙaci Gwamnatin Jihar Ogun ta biya shi kuɗi, saboda a lokacin da aka soke yarjejeniyar, katanga kawai kamfanin ya gina a filin da aka ware masa don gina wurin kasuwancin.”

Onanuga ya ce kamfanin ya samo umarnin kotu har sau biyu daga Paris a ranar 7 ga watan Maris da kuma ranar 12 ga watan Agusta ba tare da sanar da Gwamnatin Najeriya ko Gwamnatin Jihar jihar Ogun kan shigar da ƙarar ba.

Don haka ina ganin kamfanin ”ya gabatar wa kotun muhimman bayanai wajen yaudarar kotun kan jiragen shugaban Najeriya uku da aka kai Faransa domin yi musu gyara”.

“Matsayin jiragen Shugaban Ƙasa da kuma aikin da suke yi a matsayin kadarorin ƙasa, waɗanda ke da kariyar diflomasiyya, bai kamata kowacce kotun waje ta bayar da damar ƙwace su ba,” in ji shi.

Tun yaushe aka shigar da ƙarar?

A shekarar 2016 be kamfanin na Zhongshan ya shigar da ƙara, bayan da Gwamnatin Jihar Ogun ta soke kwangilar da suka cimma da kamfanin a shekarar 2007 na samar da wasu kamfanonin kasuwanci masu sauƙin haraji a jihar.

Yunƙurin kamfanin Zhongshan na sake farfaɗo da yarjejeniyar ya gamu da cikas a shekarar 2018 lokacin da kamfanin ya garzaya wasu kotunan ƙasar da buƙatar farfaɗo da yarjejeniyar.

To amma a watan Maris ɗin shekarar 2021, wata kotu ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙotun Ƙolin Birtnaiya, ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar ta biya kamfanin diyyar Dala miliyan 74.5 , amma sai Gwamnatin Jihar Ogun ta yi biris da hukuncin, ta ƙi biyan diyar.

Sannan baya ga jiragen Shugaban Ƙasar uku da aka ƙwace a Faransa, kamfanin na China ya buƙaci kotun ta ba shi damar ƙwace iko da kadarorin Najeriya a ƙasashen Birtaniya da Amurka da Belgium da Canada da Faransa da Singapoe da kuma tsibirin British Virgin Islands, Jaridar Punch ta rawaito.

Haka ma a ranar 14 ga watan Agusta, Jaridar Premium Times ta rawaito cewa wata kotun Birtaniya ta bayar da umarnin ƙwace wasu gine-gine mallakin Najeriya a birnin Liverpool da kimarsu ta kai Dala miliyan 1.7 zuwa miliyan 2.2.

Yadda Hukuncin Ya Tayar Da Ƙura a Najeriya

Wannan batu dai ya janyo ce-ce-ku-ce tare da suka ga gwamnatin Najeriyar tsakanin ‘yan ƙasar musamman ‘yan siyasar hamayya, waɗanda suka ga baiken gwamnatin ƙasar kan hakan.

Daga ciki akwai tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasar na Jam’iyyar LP, Peter Obi wanda ya bayyana ƙwace jiragen Shugaban Ƙasar a matsayin ‘cin fuska’ da gazawa jagororin ƙasar.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Obi ya ce wannan batu ya ”tona asirin gwmnatin ƙasar na ci gaba da shirinta na saya wa Shugaba Ƙasar sabbin jirage.

“Duk da irin koke-koke da sukar da aka yi wa shirin gwamnatin Najeriya na saya wa Shugaban Ƙasa jirage a wannan lokaci da ‘yan ƙasa ke cikin halin matsin rayuwa da tattalin arziki, sai kuma yanzu su ɓullo da wannan batu”, in ji mista Obi.

“Ba don yanzu da kotun Faransa ta hana Najeriya ɗaukar jiragen uku ko sayar da su ba, ‘yan ƙasar ba su da wani labari kan sayar da su ko sayo wasu”.

“Biyan kuɗin da ya kai Dala miliyan 100 don saya wa Shugaban Ƙasa jirgi – a ƙasar da ta zama cibiyar talauci ta duniya, wadda ƙananan yaranta da dama ba sa samun damar zuwa makaranta, sannan hauhawar farashin abinci ya kai kashi 40 – babban abun damuwa ne ga al’ummar ƙasar”, kamar yadda Obi ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamna Bala Mohammed Na Jihar Bauci; Ya Ce Idan Jonathan Zai Dawo Takara 2027 To Zai Jan Ye Masa

Next Post

Yadda gwamnan wata jiha a Najeriya ya dauki hanyar Hana Kiran Salla a jihar sa

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Labaran yamma tareda khadija Muhammad maitaya

Shari’ar zabe, gwamnan Kano ya garzaya kotun koli

November 22, 2023
Dan Majalisar  Dokokin Jihar Ya Sauya Sheka Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa APC

Dan Majalisar Dokokin Jihar Ya Sauya Sheka Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa APC

August 26, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media