Kungiyar matuka motocin haya na Akorikura ta Kasa reshen railway dake Murtala Mohd way a nan jihar Kano,ta jaddada Kudirinta na ci gaba da baiwa Gwamnati cikakken hadin kai wajen ganin an kara bunkasa harkokin Sufuri a fadin jihar nan.
Shugaban Kungiyar Alh. Abubakar Daniya Bala ne ya jaddada hakan a lokacin da yake Zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake titin Murtala Mohammed way.
Shugaban yace,za su baiwa Gwamnatin da Ma’aikatar Sufuri goyan bayan da suka kamata na cimma burin Gwamnatin na bunkasar tattalin arzkin Sufuri na jihar kano da kasa baki daya.
Abubakar Daniya ya bayyana cewa, rashin gurin zama na din_din_din ne babbar matsalar Kungiyoyin Direbobi da dama a jihar nan, Sakamakon Makudan kudade da fargaba da ‘Ya’yan Kungiyoyin suke fuskanta.
Shugaban yace,a don haka, Kungiyar Matuka motocin Akorikura ta kasa dake railway, a shirye take domin komawa Kasuwar Dangwauro don yin Sana’a duba da rashin wurin tsayawa na din_din_din.
Shugaban Kungiyar yace,Kofar Kungiyarsa a bude take wajen komawa Sabuwar Kasuwar Dangwauro domin kara inganta yankin ta fannoni da dama da suka kamata,Musamman wajen janyo baki da bunkasa martabar wuri Wanda da zarar an Samar da tashar motocin haya a ciki.
Shugaban ya bayyana cewa, ‘Ya’yan Kungiyar Matuka motocin haya na Akorikura ta kasa dake railway, Mutane ne masu biyayya da bin umarnin Gwamnati da na Uwar Kungiya da sauran Mahukunta yadda ya kamata.
Daniya Bala yace,ba za su gajiya ba,wajen kiraye_kiraye ga Gwamnati domin samarwa Kungiyar Matuka motocin haya na Akorikura ta kasa dake railway wajen tsayawa na din _din__din ba.
Ibrahim sani gama pyramid radio.










