• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Jami’an tsaro ne ke jawo jama’a cikin aikata miyagun Laifuka: Gwamnan Borno, kalli dalilinsa

aksam by aksam
May 7, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya haramta sayar da barasa, yayin da ya zargi sojoji da sauran jami’an tsaro da aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a birnin Maiduguri da kewaye.

Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar.

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen kaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan dabi’u.

“Na yi farin ciki da sanin cewa jami’an soji suna wajen nan, musamman sojoji, ‘yan sanda, da sauran su, domin yawancin wadannan ayyukan wa ke yin su? Wasu daga cikinsu akwai jami’an soji da aka kora da masu ci a yanzu har da fararen hula.

“Don haka, bai kamata a ƙi sukar kowane ɓangare ba a cikin wannan lamarin idan har muna son babban birnin Maiduguri da kuma jihar ta kawar da ta’addanci da sauran laifuka,” in ji Zulum.

A takaitaccen taron, Zulum ya sake kafa kwamitin tare da sake ba wa kwamitin damar kawar da duk wani nau’i na miyagun laifuka da munanan dabi’u a cikin babban birnin Maiduguri da kewaye.

Dokar hana sayar da barasa da kayan maye, a cewar gwamnan, ta samo asali ne daga yadda ake ta samun tashe-tashen hankula a tsakanin kungiyoyin da ke gaba da juna da kungiyoyin asiri da karuwanci da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ‘yan fashi da sata, wadanda suka haddasa asarar rayuka da dukiya.

Gwamnan ya hada hannu da sojoji, ‘yan sanda, Civil Defence, da wasu jami’an tsaro da dama da suka hada da civilian JTF domin shiga cikin kwamitin domin gudanar da cikakken bincike.

Da yake amincewa da aikin da ke gaban kwamitin da aka sake kafawa, shugaban kwamitin ya yi tir da tabarbarewar harkokin tsaron cikin gida a Maiduguri tare da bayyana matakin da kwamitin zai dauka nan take.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnatin Katsina taagantu kan korafi da cecekucen da ya mamaye kafafen sada zumunta

Next Post

Gwamnatin tarayya ta fadi dalilin da ya hana ɗalibai cin jarabawar JAMB

aksam

aksam

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo
Uncategorized

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

by aksam
September 5, 2026
Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Bayan harbe gomman Yan zanga-zanga, NLC tayi martani ga rundunar Yansanda

Bayan harbe gomman Yan zanga-zanga, NLC tayi martani ga rundunar Yansanda

August 3, 2024
Na zo da kyawawan shirye _shirye da za su inganta rayuwar Direbobi: sabon shugaban kungiyar Direbobi

Na zo da kyawawan shirye _shirye da za su inganta rayuwar Direbobi: sabon shugaban kungiyar Direbobi

April 22, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media