Daga Khadija Muhammad Maitaya.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da sabon jadawalin yakin neman zaben shekarar 2027, bisa tanadin Dokar Zabe ta 2026.
A cewar hukumar, jam’iyyun siyasa da ’yan takara za su fara yakin neman zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa daga ranar 19 ga Agustan 2026, sannan a kammala ranar 15 ga Janairun 2027, kwana guda kafin zaben da za a gudanar ranar 16 ga Janairu.
Haka kuma, yakin neman zaben Gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi zai fara ranar 9 ga Satumban 2026, kuma ya kare ranar 5 ga Fabrairun 2027, kwana guda kafin zaben ranar 6 ga Fabrairu.
INEC ta ce Dokar Zabe ta 2026 ta tanadi cewa yakin neman zabe ba zai fara ba sai kwanaki 150 kafin ranar zabe, kuma dole ne a dakatar da shi sa’o’i 24 kafin fara kada kuri’a. Hukumar ta gargadi jam’iyyun siyasa da ’yan takara da su bi wannan jadawali, domin duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukuncin da ya dace.
NK/NBA










