• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kotun Duniya zata yanke hukunci kan rikicin da ya shafe shekaru 125

aksam by aksam
May 19, 2025
Reading Time: 3 mins read
0
Home KOTU
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

A ranar Litinin ɗin nan ne ake sa ran babbar Kotun Majalisar Dinkin Duniya za ta yanke hukunci kan taƙaddamar da aka kwashe shekaru da dama ana yi tsakanin ƙasashen Gabon da Equatorial Guinea kan tsibirai uku na ruwa masu arzikin mai.

Ƙasashe biyu na yammacin Afirka sun yi ta cece-ku-ce a kan tsibirin Mbanie mai faɗin hekta 30 (acre 74) da wasu ƙananan tsibirai guda biyu, Cocotier da Conga, tun a farkon shekarun 1970.

Tsibiran ƙanana ne kuma kusan ba’a iya rayuwa a can, amma suna wani yanki mai arzikin mai da iskar gas.

Rikicin dai ya samo asali ne tun a shekara ta 1900, lokacin da ƙasashen Faransa da Sifaniya da suka yi musu mulkin mallaka suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Paris kan nufin samar da iyakokin kasashen biyu.

Sai dai Gabon ta yi imanin cewa yarjejeniyar da aka yi a baya ta Bata a 1974, a lokacin ta tabbatar da ikon mallakar tsibiran.

‘Takarcen takarda’

Yarjejeniyar Bata “warware duk wasu batutuwan da suka shafi ikon mallakar tsibirai da kuma ƙayyade iyakoki”, kamar yadda Marie-Madeleine Mborantsuo, Shugabar Kotun Tsarin Mulkin Gabon, ta shaida wa Kotun Ƙasa da Ƙasa ta ICJ a zaman da ta yi a watan Oktoba.

Ƙasar Equatorial Guinea ta ce Gabon ta mamaye tsibiran ne a shekarar 1972 kuma tun daga lokacin ta mamaye su ba bisa ƙa’ida ba.

Lauyoyin Equatorial Guinea sun yi watsi da yarjejeniyar Bata a zaman da aka yi a watan Oktoba, inda suka ce ba zato ba tsammani Gabon ta fitar da takardar a shekara ta 2003, abin da ya bai wa kowa mamaki.

“Babu wanda ya gani ko ya ji labarin wannan babban taron.” kamar yadda Domingo Mba Esono, Mataimakin Ministan Ma’adinai da Sinadarin Hydrocarbons daga Equatorial Guinea, ya shaida wa alƙalan kotun ta ICJ.

“Bugu da kari, takardar da aka gabatar ba ta asali ba ce, sai dai kwafin da ba a tantance ba kawai,” in ji Esono.

Philippe Sands, lauya mai wakiltar Equatorial Guinea, ya yi watsi da Yarjejeniyar Bata a matsayin “tarkacen takarda”.

‘Ba a adana takarda da kyau ba’

“Ana rokon ku da ku yanke hukuncin cewa wata ƙasa za ta iya dogaro kan kwafin kwafin wata takarda da ake iƙirarin akwai ta, wacce ba za a iya samun ta ainihi ba, kuma wadda ba a ambace ta ba ko kuma wani abu da za a iya dogaro kanta a tsawon shekaru talatin,” in ji Sands.

Tun a 2003 Equatorial Guinea take neman ainihin kwafin takardar yarjejeniyar Bata, kuma har ya zuwa yanzu ba ta yi nasara.

Mborantsuo ya yarda cewa “abin baƙin ciki shi ne, babu ɗaya daga cikin ɓangarorin biyu da zai iya samun ainihin daftarin takardar”, lura da cewa an zana ta ne kafin zuwa kwamfutoci da sauran hanyoyin tattara bayanai.

“Ba a adana su yanda ya kamata ba saboda abubuwa da dama kamar – yanayi mara kyau, da rashin ƙwararrun ma’aikata da rashin fasaha,” in ji Mborantsuo.

Ba kamar sauran ƙasashen da ke bayyana a gaban kotun ICJ da ke birnin Hague wadda ke shari’a kan taƙaddamar da ke tsakanin kasashe ba, Guinea da Equatorial Guinea sun amince da bukatar alƙalan kotun da su yanke hukunci a ƙoƙarin da ake yi na ganin an sasanta.

Ƙasashen biyu sun buƙaci kotun ta yanke hukunci kan wanne takardu ne za a yi aiki da su – yarjejeniyar Paris ta 1900 ko yarjejeniyar Bata ta 1974.

Kotun ICJ ba za ta yanke hukunci kan kasar da ya kamata a bai wa ikon mallakar tsibiran ba.

“Muna da yaƙinin hukuncin kotun zai taimaka wa ƙasashenmu wajen warware taƙaddamar da ke tsakaninsu kan batun haƙƙn mallaka da iyakoki, tare da samar da dawwamammen ginshiki wajen bunƙasa dangantakarsu,” in ji Esono na Equatorial Guinea.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnan Borno ya roki gwamnatin tarayya Abu ɗaya domin yanta Garin Marte daga yan Boko Haram

Next Post

Sakon Taya murna ga Dan Alhaji Kabiru Sanda ta Samun Karuwar ‘Da Daga Babale Sanda

aksam

aksam

RelatedPosts

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

by Khadija Maitaya
August 7, 2026
Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar  (ADC) Na Kasa
KOTU

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

by aksam
April 30, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

by aksam
April 30, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

by aksam
April 22, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Wani Dan Majalisar Jihar Kano Ya Sauya Sheka Daga NNPP Zuwa APC

Wani Dan Majalisar Jihar Kano Ya Sauya Sheka Daga NNPP Zuwa APC

May 12, 2025
Da DUMI-DUMI: Rundunar Yan sanda ta shirya samar da tsaro ga masu gudanar da zanga-zanga na tsawon kwanaki 10

Yanzu-yanzu I G na kasa ya bada umarni mai tsauri kan masu zanga-zangar kuncin rayuwa

August 1, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media