• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Ma’aikatar Shari’a Ta Jihar Kano Ta Ziyarci Alkalin Alkalai na Jihar

Khadija Maitaya by Khadija Maitaya
July 23, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Khadija Muhammad Maitaya

Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta ziyarci Alƙalin Alƙalai na jihar Kano, Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, domin tattauna wa kan yadda za a magance matsalolin da ake fuskanta a harkokin Shari’a, tare da daƙile jinkiri a shari’a a kotuna, tare da saurin yanke hukunci a kan shari’ar bashi da gado da sauransu.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Ziyarar shugabannin hukumar shari’ar ta gudana ne a larabar nan, inda bangarorin biyu suka tattauna mahimman batutuwa a ofishin Alkalin Alkalan na jihar Kano, Dr. Tijjani Yakasai.

Tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne a kan yadda za a lalubo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a harkokin shari’a, da kuma saurin warware shari’ar bashi da ta auratayya da sauransu, domin kara samar da sauki a tsakanin maƙaraya.

Da yake karin bayani a yayin ziyarar, shugaban hukumar shari’a ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ce akwai bukatar a rinka gaggawar yanke hukunci a kan shari’un da suke bukatar gaggawa musamman ma irin na fadan daba, da kwacen waya da kuma ta’ammali da kayan maye, duba da yadda matsalar ke ci gaba da addabar jama’a a jihar Kano.

Shima a nasa banagren, Alkalin Alakalai na jihar Kano, Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, ya ce matukar ana son a kawo karshen yawaitar aikata manyan laifuka a sasan jihar nan musamman ma na kisan kai, sai Gwamnati ta tashi tsaye wajen zartas da hukunci a kan mutanen da kotu ta yankewa hukuncin kisa.

Dr. Tijjani Yusif Yakasai ya kuma ce tara masu ruwa da tsaki wajen zama na musamman domin fito da matsalolin da ake fuskanta a harkar shari’a da jami’an tsaro, ka iya taimakawa wajen magance kashe rayuka a sassan jihar.

A nasa jawabin, Kwamishina na biyu a hukumar shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali Danabba, ya ce hukumar za ta kara himma wajen ganin an dakile sha da dillancin miyagun kwayoyi a fadin jihar nan, domin tabbatar da gyaruwar tarbiyyar matasa.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa a yayin ziyarar dai shugaban hukumar shari’ar ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, na tare da Kwamishina na biyu a hukumar Gwani Dahiru Yakasai, da Daraktocin hukumar da ma’aikata dai sauransu.
DFM/NBA

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da Jadawalin yakin neman zaben shekarar 2027

Next Post

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

Khadija Maitaya

Khadija Maitaya

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Hur man kontaktar Partyspins Casino support

April 22, 2025
Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji’un Allah Ya Jikan Haruna Dauda Biu Wakilin Muryar Amurka Na Jihohin Borno Da Yobe

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji’un Allah Ya Jikan Haruna Dauda Biu Wakilin Muryar Amurka Na Jihohin Borno Da Yobe

May 18, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media