• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

HON ABDULMUMIN JIBRIN KOFA, PHD YA SHIRYA TARON ADDU’A KAN NASARAR KOTU, YA TALLAFA WA MUTUM 10,000

aksam by aksam
November 13, 2023
Reading Time: 1 min read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Zakariyya Jigirya

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji/Kiru, Rt Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, PhD, a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023, ya shirya taro na musamman wanda ya haɗa sama da mutum 10,000 domin yin addu’o’i a garinsa na Kofa da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Ɗan majalisar mai hawa huɗu ya shirya taron ne domin ya gode wa Allah saboda nasarar da ya samu a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe da ta Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja a kwanakin baya, da kuma raba wasu kayan tallafi ga ’yan mazabarsa.

A yayin kasaitaccen taron dai, an bayar da tallafi ga ’yan mazabar su 10,000 maza da mata. Bugu da ƙari, an ba mutanen tallafin kuɗi da kayan sanaa da motoci da kayan abinci da sutturu da kuma sauran kayan amfanin yau da kullum.

Kazalika, an yi addu’a ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin neman Allah Ya ba shi nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta Ƙoli, da sauran ’yan majalisar Kano na NNPP da suka yi nasara a kotu, da ma fatan nasara ga waɗanda ba a kai ga yanke nasu hukuncin ba. Sannan an yi wa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, addu’ar neman Allah Ya ja kwanan sa, Ya ƙara masa lafiya da kuma biya masa bukatunsa.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Al’ummar Hayin Dan Mani Dake Karamar Hukumar Igabi A Jihar Kaduna: Sun Bayyana Yadda Wata Bola Take Yin Barazana Da Lafiyarsu

Next Post

Inna lillah wa ilaihin raji’un !!

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Strategier för att Välja de Bästa Videoslots med Bonus: En Expertguider

April 21, 2025
An Sako Mahaifiyar Mawaki Rarara Da Aka Sace

An Sako Mahaifiyar Mawaki Rarara Da Aka Sace

July 17, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media