• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu Ta Yi Wa Gwamnonin PDP Martani Akan Matsalar Tattalin Arziki

aksam by aksam
February 15, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home SIYASA
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Bayan sun kwatanta halin da tattalin arzikin Najeriya ya ke ciki da irin na ƙasar Venezuela.

RelatedPosts

Dawo da tallafin man fetur

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya ce duk da dai tattalin arzikin Najeriya na fuskantar ƙalubale, kwatanta shi kafaɗa-da-kafaɗa da na Venezuela da gwamnonin PDP suka yi, rashin adalci ne ainun.

“Muna bayyana cewa duk da ƙasar mu na fuskantar wasu matsaloli, waɗanda kuma wannan gwamnati ta Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin magance su, to kuma matsalolin mu ko kusa ba su kai ga na Venezuela ba, kamar yadda gwamnonin PDP suka rufe ido suka faɗa,” haka Idris ya bayyana a cikin wata sanarwar da aka raba wa PREMIUM TIMES a ranar Talata.

“Tattalin arzikin Najeriya har yanzu ya na da ƙarfi sosai, kuma ana sa rai da kyakkyawan hasashen cewa zai bunƙasa da ƙarin kashi 3% bisa 100% cikin wannan shekarar.

“Tattalin arzikin mu na bayar da gudunmawar lamuni ga masu ramce a cikin gida da waje.”

A ranar Litinin ce dai gwamnonin PDP suka gudanar da taro a Abuja, inda suka tattauna batutuwa, musamman waɗanda suka shafi matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki, wadda ta haifar da matsalar tsada da raɗaɗin tsadar rayuwa.

Bayan kammala taron, sun bada sanarwar cewa sun amince kowace jiha a ba ta damar kafa ‘yan sandan jiha, domin a samu a shawo kan ƙalubalen matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Minista Idris ya ce muna maraba da shawarwarin da suka bayar waɗanda ba na son rai ba, domin ganin an magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki,” inji Idris.

Daga nan kuma ya fara ragargazar gwamnonin da cewa sun taimaka wajen haifar da matsalar tattalin arziki.

“A matsayin su na shugabanni a gwamnatocin jihohi, gwammonin PDP su na da ‘yancin bayyana matsayar su kan duk wani abu da ya shafi ƙasar nan.

“ ya kamata a ce masu shiga sahun gaban inganta tattalin arziki ne, samar da yalwa a ƙasa ga ‘yan ƙasar a jihohin su, a ce kuma sun koma su na furka kalaman ƙage da shaci-faɗi kan Najeriya, har su na kwatanta matsalar tattalin arzikin Najeriya da irin matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin Venezuela.

“Mu na son mu bayyana cewa duk da dai tattalin arzikin mu na fuskantar ƙalubale, amma ki kusa ba daidai ba ne a kwatanta matsalar Venezuela da ta Najeriya.

“Ya yin da gwamnatin tarayya ke biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikata kan kari, kuma harkokin gwamnati na tafiya dai-dai-wa-dai-da, ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi gwamnonin PDP abin da suka yi da kuɗaɗen da ake ba su. Saboda akwai rahoton bincike mai nuna cewa yawancin jihohin PDP sun kasa biyan ‘yan fansho kuɗaɗen su na tsawon watanni da dama, haka albashin ma’aikata ma wasu ba su biya yadda ya kamata. Gwamnonin PDP na ƙin biyan garatutin ma’aikatan da suka yi ritaya.

“Haka kuma wasu gwamnonin PDP ɗin har yau sun kasa ma biyan Naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, shekaru huɗu da gwamnatin tarayya ta fara amfani da tsarin,” inji Minista Idris.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kungiyar Masu Gidajen Bride A Najeriya Zasu Fara Yajin Aiki

Next Post

Shahararren Dan Wasan Kwallon Kafa Dake Buga Wasa A Kungiyar Kwallon Kafa Ta Al Nassr, Cristiano Ronaldo Ya Buga Wasannin Dubu (1000) A Tarihi

aksam

aksam

RelatedPosts

Atiku Ya Nemi Tinibu Ya Fadi Inda Ya Saka Tiriliyan 30 na Tallafi Mai Da Ya Cire.
SIYASA

Dawo da tallafin man fetur

by Khadija Maitaya
August 26, 2026
Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa
SIYASA

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

by Khadija Maitaya
July 28, 2026
Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin
SIYASA

Mataimakin shugaban kasa zai jagoranci tawaga zuwa Jamhuriyyar Benin

by Khadija Maitaya
July 23, 2026
Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce
SIYASA

Daukar DanKwankwaso Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Kano A NDC Ya Jaho Ce-ce-ku-ce

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yadda Y’an sanda sun kama ‘yan fashi da masu garkuwa 14

January 15, 2024
Gwamnan Kano zai Gina masallacin Juma’a sadaukar wa ga wadanda suka rasu a rikicin BUK da mutanen Rimin Danzakara

Gwamnan Kano zai Gina masallacin Juma’a sadaukar wa ga wadanda suka rasu a rikicin BUK da mutanen Rimin Danzakara

February 7, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media