Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni sun fara cimma matsaya kan batun kafa yan sandan jihohi da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka ga masu ɗauko rahoto a fadar shugaban kasa ranar Alhamis
Idris ya ce an cimma matsayar kafa ƴan sandan jihohin ne a taron Shugaba Tinubu da gwamnoni wanda aka yi ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024.
A cewar Ministan, a halin yanzu za a ci gaba da tattauna yiwuwar kafa tsarin yadda ‘yan sandan jihohi zasu kasance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ya kuma ƙara da cewa nan gaba za a kira taruka da dama domin lalubo hanyoyon da za a bi domin kafa wannan runduna da nufin magance matsalar tsaron da ta addabi ƙasa.
Mohammed Idris ya ce: “Amma a yanzu an fara tattaunawa kan batun kirkiro ƴan sandan jihohi, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi sun fara tunanin kafa ƴan sandan jihohi












