• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Ganduje yayi martani ga shugaba Tinubu bayan yi masa tayin jakadanci a kasashen Afirika

aksam by aksam
August 15, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
473
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa shugaban jam’iyyar APC mai mulki na ƙasa, Abdullahi Ganduje tayin muƙamin jakada a kowace kasa ta Afrika, kamar yadda sahihan majiyoyi su ka bayyana.

Jaridar DAILY Nigerian ta ce majiyoyi masu tushe wadanda su ka buƙaci a  sakaya sunayensu sun tabbatar mata da cewa Tinubu ya fara wakilta Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya isar da “mummunan labarin” ga Ganduje.

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

A cewar majiyoyin, Akpabio ya shaida wa Ganduje cewa tayin muƙamin ambasada da Tinubu ya yi masa wata dabara ce ta kare shi daga shari’o’i na cin hanci da rashawa da ya ke fuskanta a Kano a halin yanzu.

Ganduje, wanda faifan bidiyonsa na cin hanci da rashawa a 2018 ya janyo masa ba’a da tsokana, yana fuskantar tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa tare da matarsa, dansa da sauran masu hannu da shuni na sama da Naira biliyan 50 a jihar Kano.

Sai dai wasu majiyoyi na cikin gida sun ce Ganduje ya yi gunaguni kuma ya yi watsi da tayin shugaban kasar, inda ya bayyana cewa tuhumar da ake yi masa “ba mai dorewa ba ce” kuma zai ci nasara a shari’arsa a kotu.

“Duk irin goyon bayan da na yi wa shugaban kasa, sakaiyar da zai min kenan? ban da haka, na tsufa da yawa da zan je wata ƙasa a matsayin jakadanci. Duk tuhume-tuhumen da ake yi na karya ne, kuma zan ci nasara a shari’a ta a kotu,” an jiyo Ganduje yayin da ya ke mayar da martani ga Akpabio.

A cewar majiyoyin, daga baya shugaban kasar ya sanar da Ganduje shirin diflomasiyya tare da ba shi zabin “kowace kasa a Afirka”

Sai dai wasu majiyoyi sun ce shugaban ya yi masa zabi uku a Afirka, Asiya da Nahiyar Turai.

Amma kuma wasu majiyoyin sun baiyana cewa shi Tinubu ya fi son ya tura Ganduje a kasar Chadi a matsayin jakada, inda ta kara da cewa “babu wata kasa da ta san ciwon kanta a Nahiyar Turai da Asia da za ta karbi Ganduje a matsayin jakada idan aka yi duba da dumbin tuhume-tuhume na cin hanci a kan sa”.

Sai dai kuma majiyoyin sun tabbatar da cewa Ganduje ya dage sai ya riƙe muƙamin sa na shugaban jam’iyya, inda aka ce ya na ta kai gwauro ya kai mari wajen manyan makudantan Tinubu, irin su Bisi Akande domin su taushi shugaban kasa ya janye wannan kuduri na sa.

Share189Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Ƙarancin Abinci, Hedkwatar Tsaro ta tura rundunar soji ta bawa manoma kariya a wasu jihohin Arewa

Next Post

Tsananin rayuwa ta sa wata baiwar Allah ciyar da yayan ta da dusar kaji

aksam

aksam

RelatedPosts

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala
LABARAI

Shirye – Shiryen Fara Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin 2026, Na Jihar Kano Ya Kammala

by aksam
April 17, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID
Uncategorized

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

by aksam
April 17, 2026
Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka
Uncategorized

Araqchi Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matsaya Ka

by aksam
April 11, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Mazauna Unguwar Kofar Mazugal Sun Yi Kira Ga Hukumar (KNUPDA) Da Kuma Jami’an Hukumar Civil Defence Dasu Gaggauta Rushe Wani Ofishin Wucin Gadi Da Aka Kafa A  Yankin

Mazauna Unguwar Kofar Mazugal Sun Yi Kira Ga Hukumar (KNUPDA) Da Kuma Jami’an Hukumar Civil Defence Dasu Gaggauta Rushe Wani Ofishin Wucin Gadi Da Aka Kafa A Yankin

April 2, 2026
Jam”iyar NNPP ta bayyana matsayartakan batun dakatar da Gwamnan Kano da Dan takararta na shugaban kasa

Jam”iyar NNPP ta bayyana matsayartakan batun dakatar da Gwamnan Kano da Dan takararta na shugaban kasa

July 9, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media