Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta yi fatali da dakatarwar da wani tsaginta ya yiwa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf
Jam’iyyar ta kuma yi fatali da korar da aka yiwa jagoranta na ƙasa kuma ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Rabiu Musa Kwankwaso
Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hashim Dungurawa, ya bayyana matakin dakatarwar da korar a matsayin haramtacce
NNPP ta bayyana dakatarwar a matsayin abin dariya, inda ta dage cewa wasu korarrun ƴaƴan jam’iyyar NNPP ne suka aikata hakan, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Ya kuma yi zargin cewa wasu ne suka ɗauki nauyin waɗanda suka dakatar da Gwamna Abba tare da korar Kwankwaso daga jam’iyyar.











