Tsanani da kuncin yanayi ne da ka iya saka mutane su shiga wani hali da ka iya can a musu akalar su har ma su aiwatar da abun da ba haka ransu ya soba kamar yadda wata mata a jihar Akwa Ibom ta dukufa wajan ciyar da yayan ta da abincin kaji saboda tsananin talauci.
A zantawarta da manema labarai matar mai suna Grace Eseneowo dake zaune a Okon Eket a Jihar Akwa Ibom tace tana zaune ne a gidan mahaifinta kuma tana aiki inda ake biyanta 15, 000 a kowanne wata, wanda ba zai iya saya mata abincin da zata ciyar da ‘yayan nata ba.
Bayan yada labarin matar a kafar sadarwa Queen Praise Uzoma ta yi nasarar samar wa da matar taimakon Kudi har Naira naira miliyan guda da dubu 400 domin kula da ‘yayan na ta.
Daga bisani uwargidan gwamnan jihar Akwa Ibom ta samu labarin inda ta yi alkawarin taimaka wa mata, bayan mika mata taimakon gaggawa na naira dubu 500 domin samun matsuguni na kan ta.
Jihar Akwa Ibom na daya daga cikin wadanda suka fi samun kudade daga gwamnatin tarayya saboda mallakar arzikin man fetur.










