• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gamayyar kungiyoyin Fulani sun magantu bayan tsare shugaban Miyetti Allah fiye da kwanaki 10

aksam by aksam
February 4, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Wasu Kungiyoyin Fulani sun yi barazanar kai Gwamnatin Tarraya kotu, kan ci gaba da rike shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Abdullahi Bello Badejo, bayan kwanaki 10 da kama shi da suka yi.

Kungiyoyin Fulani na FAYAN da FANAM sun koka ne a wata sanarwa da suka fitar da ke cewa ci gaba da tsare Badejo da jami’an tsaro ke yi bayan kwanaki 10 da kama shi, na nuni da cewa gwamnati ba ta da niyar gurfanar da shi a gaban kuliya a nan kusa.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Sanarwar wacce ta fito ta hannun Ambasada Mohammed Tasi’u Suleiman, ta ce rundunar sojoji Najeriya da aka ce su ne suka kama Badejo ba ta da hurumin tsare duk wani mutum fiye da sa’o’i 24.

Kungiyoyin sun yi kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sa baki tare da ba da umurnin a gaggauta sakin shugaban kungiyar makiyayan.

Abdulkarim Bayero yana daya daga cikin shugabanin matasa na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, ya kuma ce Fulani da aka tuntuba suna goyon bayan wannan kungiyar sa-kai da Badejo ya kafa, domin ya taimaka wajen kawar da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya, kuma kungiyar za ta yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro a yankin da suke.

Shi kuwa shugaban Kungiyar Fulani Cattle Breeders MACBAN Alhaji Usman Ngenzarma ya ce, kungiyoyi irin nasu suna da hurumin kafa kungiyoyi amma fa sai sun hada da samun izini wuri gwamnatin jiha ko na tarayya idan bukatar hakan ta taso.

Ngenzarma ya ce ya kamata a yi la’akari da yawan kiraye-kiraye da ake
yi a fannoni daban-daban na kasar kan a kafa ‘yan sandan jihohi domin a taimaka wajen shawo kan rashin tsaro da ya addabi kasar, kuma wannan kira ne mai kyau.

Amma ga kwararre a fanin tsaro, Dokta Yahuza Ahmed Getso, yana ganin akwai abin dubawa a matakan da Badejo ya dauka wajen kirkirar kungiyar sa-kai da ya yi.

Getso ya ce ya kamata Badejo ya tuntubi sauran kungiyoyin Fulani, sannan kuma ya kamata a ce wata hadaka ce aka samu tsakanin kungiyoyin sa-kai da su kungiyoyin Fulani a karkashin jagoranci na tsarin tsaro na jihar.

Getso ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban na kasa da ya ce kungiyar na Fulani zalla ne, ya kamata a ce ya sanar da hukumomin tsaro a matakin kasa wadanda za su iya tunanin cewa mene ne dalilin da ya sa za’a kafa irin wannan kungiyar ta sa-kai kafin ya kaddamar da kungiyar.

Tuni gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya musanta cewa yana da hannu wajen kafa kungiyar ‘yan banga da Abdullahi Bello Badejo ya kaddamar a jihar Nasarawa kwanan nan.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

A fakaice Amurka ta fara kaiwa kasar Iran hare-hare

Next Post

Yadda tattabara ta nemi hada yaki tsakanin wasu manyan kasashen jarfata

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

Anci gaba da rabon tallafin Naira 100,000 duk wata ga matasa 1,300 a Kano ta Arewa

July 28, 2026
Majalisar ministocin Burkina Faso ta tsawaita waadin mulkin Soji a kasar

Majalisar ministocin Burkina Faso ta tsawaita waadin mulkin Soji a kasar

May 25, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media