• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Jam”iyar Biden na farbar rasa kujerar shugaban kasa a zaben Amurka

aksam by aksam
June 28, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Yayin da yake rage watanni biyar kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Amurka, manyan ‘yan takarar shugabancin ƙasar, Shugaba mai ci, Joe Biden, da tsohon Shugaba, Donald Trump sun tafka muhawararsu ta farko a birnin Atalanta na jihar Florida.

‘Yan siyasar yi cacar-baki kuma sun riƙa zargin junansu da yin ƙarerayi yayin da suke tattauna batun manufofin harkokin wajen ƙasar, da tattalin arziƙi da batun zubar da ciki.

Ana kallon wannan zazzafar karawar da dattijan ‘yan takarar suka yi a matsayin manuniya kan yadda babban zaɓen watan Nuwamba mai zuwa zai kasance mai zafi.

Trump ya soki Biden kan tattalin arziƙi da kuma tsare-tsaren manufofin harkokin wajensa, yayin da Biden ya taɓo batun laifin da kotu ta samu Trump da shi da kuma batun yunƙurin da ya yi na juya sakamakon zaɓen shekarar 2020.

Dattijan ‘yan siyasar biyu, waɗanda suka riƙa zagin juna, su ne mutanen da suka fi tsufa da suke neman shugabancin Amurka da aka taɓa gani a tarihin ƙasar.

Mutanen biyu sun yi muhawara mai zafi kan dokokin zubar da jiki da batun kwararar baƙi, da batun yaƙin Ukraine da na Gaza, da kuma batun tafiyar da tattalin arziƙi da na wasan Golf da kowanensu ke bugawa.

Saboda yadda ƙwazon ’yan siyasar biyu ya bambanta yayin muhawarar, gwiwoyin wasu ’yan jam’iyyar Democratic sun fara yin sanyi, kuma hakan zai sa wasu masu kaɗa ƙuri’a su fara nuna damuwa kan cewa Biden, mai shekara 81, tsufansa zai kawo tangarɗa ga nasarar sabon wa’adin mulkinsa.

Wani babban mai bai wa Biden gudunmuwar kuɗin kamfe, wanda ba ya so a bayyana sunansa, ya soki shugaban kuma ya ce muhawarar ta nuna “bai cancanta ba”. Haka nan ya ce yana sa ran cewa za a fara sabon kiraye-kiraye kan ka da Biden ya sake yin takara gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa a watan Agusta.

Daga bisani Mataimakiyar Shugaban Ƙasar, Kamala Harris ta amince cewa Biden ya fara muhimmiyar muhawarar “babu karsashi”, inda ya fafata da babban abokin hamayyarsa, ko da yake ta ce jam’iyyarsu ta Democratic ta gama muhawarar da “ƙarfin gwiwa.”

“Ya fara babu karsashi wanda kowa ya san haka. Ba zan iya kare wannan ba,” kamar yadda ta bayyana wa kafar yaɗa labarai ta CNN, bayan muhawarar da Biden ya nuna rashin karsashi kuma ya sanya shakku a zukatan jama’a kan sake tsayawarsa takara.

Za a sake yin muhawara ta biyu kuma ta ƙarshe tsakanin manyan ’yan takarar biyu a watan Satumba mai zuwa.

A watan Nuwamba ne za a gudanar da babban zaɓe a Amurka, kuma Shugaba Biden ne ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar Democratic, yayin da tsohon Shugaba Trump yake yi wa babbar jam’iyyar adawa ta Republican takara.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Bayan kai hari garin Kahutu Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Next Post

NLC tayi martani kan kokarin wasu gwamnoni na kassara maaikata

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Gwamnan Ondo, Akeredolu Ya Rasu Yana Da Shekaru 67 A Duniya

Gwamnan Ondo, Akeredolu Ya Rasu Yana Da Shekaru 67 A Duniya

December 27, 2023
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

June 22, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media