• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

NLC tayi martani kan kokarin wasu gwamnoni na kassara maaikata

aksam by aksam
June 29, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, ta mayarwa da wasu gwamnomin jihohin ƙasar man martani kan ƙoƙarin da suke na ganin an bai wa kowacce jiha damar yanke abin da za ta iya biya a matsayin mafi ƙarancin albashi, saɓanin ƙokarin da ake yi na ganin an amince da farashi na bai ɗaya.

Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewar da alama gwamnonin ba su fahimci tsari da dokar albashi mafi ƙanƙancin ba.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Kwamared Benjamin Anthony, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewar albashi mafi ƙanƙanata ake son a biya, wanda kuma a duniya ma idan aka kayyade albashin mafi ƙaranci da za a biya, babu wani sashe ko jiha da za ta biya ƙasa da yadda aka ƙayade, tunda doka ce ta bai ɗaya, wadda ita kanta ƙungiyar ƙwadago ta duniya ta amince da ita.

wamared Benjamin Anthony, ya kara da cewar “rashin adalci ne da ake fama da shi a kasar, a ce ga gaskiyar abin da tattalin arziki ke cewa, a ce ga albashi mafi karanci da za a biya, amma a ce ba za a bi ba, ko da gwamnati ta ce zata bayar da naira dubu sittin da biyu (N62, 000) mun yi tambayar nawa ne kudin mai a ciki ?, nawa ne kudin mota nawa ne kudin makaranatar yara?, nawa ne kudin haya? inji shi.

Ya Kuma ja hankalin gwamnomi da ita kanta gwamnatin Najeriya da cewar akwai bukatar su duba halin da yan kasar ke ciki, da ya sa suka bukaci mafi karancin albashi na naira dubu ɗari biyu da hamsin, wanda suka ce a hakan ma ba lallai ta biya buƙatar da ake so ba.

“ Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, sun ce za su biya dubu stittin da biyu, mu kuma mun ce sai dubu dari Biyu da hamsin, idan ka lura yanzu nawa ne kudin buhun shinkafa? Ya kai wajen Naira dubu Taminin to kaga kenan albashin da ake cewa za a biya mafi karanci ba ma zai iya saya wa ma’aikaci ko rabin bushun shinkafa ba.

Yanzu haka dai magana na hannun shugaban ƙasar Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, don haka kungiyar ta ce tana jiran ta ga matakin da zai ɗauka, wanda daga nan za su fitar da tasu mastayar.

Maratanin ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriyar na zuwa ne, bayan da wasu daga cikin gwamnonin jihohin ƙasar ke cewar ba za su iya biyan ko da Naira dubu 60 ko dubu 62 da gwamantin ƙasar ta yi wa ƴan ƙwadagon tayi ba a msatyin albashi mafi karanci.

Sai dai wasu daga cikin gwamnonin ƙasar irin su na Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar Gwamna Nasiru Idris Ƙauran Gwandu ya ce a shirye yake da ya biya ko nawa aka aminceda shi a mastayin mafi ƙarancin albashin.

 

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Jam”iyar Biden na farbar rasa kujerar shugaban kasa a zaben Amurka

Next Post

Mutane takwas sun rasa rayukansu bakwai na asibiti sanadiyar rushewar bene mai hawa daya

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

At the 2-Day Online Media Retreat in Dutse, Jigawa State.

At the 2-Day Online Media Retreat in Dutse, Jigawa State.

January 16, 2026
Shugaban Hukumar Gudanarwar UBRBDA, Barayan Bauchi, Ya Yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Kan Ware Naira Tiriliyan 1.2 Da Aka Saka Cikin Bankin Manoman Najeriya

Shugaban Hukumar Gudanarwar UBRBDA, Barayan Bauchi, Ya Yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Kan Ware Naira Tiriliyan 1.2 Da Aka Saka Cikin Bankin Manoman Najeriya

August 23, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media