Mun yi Allah wadai da duk wani mataki da zai cutar da fararen hula ko ya sabawa dokokin kasa da kasa, tare da nuna damuwa matuka kan ci gaba da tashin hankali. Muna adawa da rawar da wasu bangarori ke takawa wajen ƙara tayar da rikicin.
Muna kira ga Isra’ila da ta saurari ƙarfafan kiraye-kirayen da al’ummar duniya ke yi, ta dakatar da hare-harenta a Gaza nan da nan, ta tabbatar da cikakken zaman lafiya mai dorewa cikin gaggawa, tare da dakile tabarbarewar rikicin jin kai.










