• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Bincike ya gano adadin mutanen da suka mutu a mulkin Tinibu sun…..

Ƴan Najeriya dubu 5 ne suka mutu a shekara guda na mulkin Tinubu

aksam by aksam
May 28, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ƴan Najeriya dubu 5 ne suka mutu a shekara guda na mulkin Tinubu

Wani bincike da kafafen yada labarai na Najeriya da kungiyoyi suka gudanar ya nuna cewa ayyukan ta’addanci sun hallaka mutane 4,500 yayin da aka yi garkuwa da wasu dubu 7 cikin shekara guda tak karkashin mulkin Bola Ahmad Tinubu.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Yayin jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun bara lokacin da aka rantsar da shi, shugaban na Najeriya ya sha alwashin tunkarar matsalolin ta’addanci da kuma rashin tsaro gadan-gadan.

Wannan ba shi ne karon farko da shugaban ke yiwa ‘yan Najeriya alkawari kan magance matsalar tsaro ba, don kuwa ya kasance cikin manyan batutuwan da yake nanatawa a wajen yakin neman zabe.

To sai dai, shekara guda bayan darewarsa karagar mulki, a iya cewa babu wani sauyi na azo a gani a bangaren tsaro, illa ma dai sake sabon salon kai hare-hare da ‘yan bindiga musamman a arewacin kasar suke dauka, yayinda kungiyar Boko Haram tsagin Ansaru ke ci gaba da samun karfi.

Cikin makon da ya gabata sai dai kungiyar ta yi garkuwa da mutane 160 a jihar Neja, a wani hari da ba’a taba ganin irinsa a jihar ba.

Kungiyar ACLED mai tattara kididdigar kisa ko kuma mutanen da aka yi garkuwa da su ta ce bayananta sun nuna cewa mutane 4,556 ne suka rasa rayukansu sai wasu 7,086 da aka yi garkuwa da su a tsakanin ranakun 29 ga watan Mayun bara zuwa 11 ga watan Mayun da muke ciki.

Duk da alwakurran da shugaban yayi, da kuma ikirarin yaki da ta’addanci da manyan hafsoshin tsaron kasar keyi na yaki da ta’addanci, har yanzu matsalolin rashin tsaro na ci gaba da zama kanun labarai a gidajen jaridu.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Wasu kasashen Europe uku sun amince da kasar Palastinu

Next Post

Majalisar Dokoki ta nemi sanata Abdul Ningi ya dawo bakin aiki

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Gaskiya ta fito gameda shirin NNPCL na kara farashin Man fetur

February 9, 2024
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Jami’an EFCC Sun Cafke Jami’in Tsaro Kan Zargin Safarar Zinaren Naira Biliyan 4.4 A Kano

June 13, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media