Daga Hassan Umar Gwammaja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta sanar da kama wani jami’in tsaron filin jirgin sama, Ali Baffa, tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a safarar ɗanyen zinare da kuɗaɗen ƙasashen waje ta haramtacciyar hanya a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
A cikin wata sanarwa da ofishin EFCC na shiyyar Kano ya fitar, hukumar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin wani aikin sa ido da jami’anta suka gudanar a filin jirgin, sakamakon ƙara tsaurara matakan yaƙi da safarar albarkatun ƙasa da manyan kuɗaɗe ta tashoshin jiragen sama na ƙasa da ƙasa.
Binciken farko ya nuna cewa Ali Baffa, wanda ke aiki a sashen tsaron jiragen sama (AVSEC), ya yi yunƙurin fitar da sandunan ɗanyen zinare masu nauyin kilo 22.2, waɗanda darajarsu ta haura Naira biliyan 4.4.
Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Shugaban Koriya Ta Kudu Hukuncin Daurin Shek
EFCC ta ce ana zargin jami’in ya ɓoye zinaren domin kauce wa binciken tsaro, tare da shirin miƙa su ga wasu fasinjojin da za su tafi ƙasashen waje domin a fitar da su daga Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.
Ci gaba da bincike ya kai ga kama Aushabu Nasidi, wanda ake zargi da samar da zinaren. A lokacin da aka kama shi, jami’ai sun samu kuɗaɗen ƙasashe daban-daban a hannunsa, ciki har da Riyal na Saudiyya, Lirar Turkiyya, Dinar na Kuwait, Peso na Philippines da wasu nau’ikan kuɗaɗen ƙasashen duniya.
Haka kuma, binciken ya kai ga cafke Mukhtar Muhammad Dan Zaria, wanda ake zargin shi ne ya bai wa Nasidi zinaren da aka yi yunƙurin safararsu.
A cewar EFCC, yayin amsa tambayoyi, Dan Zaria ya amsa cewa ya yi safarar kimanin kilo 40.2 na zinare tsakanin ranar 1 zuwa 11 ga watan Yunin 2026 ta amfani da irin wannan hanya.
Hukumar ta ce dukkan waɗanda ake zargin na tsare a hannunta, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.










