Daga: Hassan Umar Gwammaja
Hukumar Tsaron ta Farar Hula ta Kasa (NSCDC) reshen jihar Kano ta sallami ma’aikatan sa-kai biyar daga aiki bisa zargin rashin da’a da rashin ƙwarewar aiki da kuma rashin ladabi.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Yakubu Mubarak Yusuf, Isma’il Muhammad, Adamu Auwalu, Abdulrazaq Suleiman da kuma Ahmad Sarki.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar NSCDC a Kano, Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce Kwamandan NSCDC na jihar Kano, Mohammed Agalama, ya amince da sallamar ma’aikatan bayan nazarin laifukan da ake zarginsu da aikatawa, waɗanda aka gano sun saɓa wa ƙa’idoji, ɗabi’u da kuma matakan gudanar da ayyukan hukumar.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an ƙwace dukkan kayan aiki, kayan sawa na aiki, katunan shaida da sauran kayayyakin da ma’aikatan ke amfani da su.
Kwamandan ya umarci kwamandojin yankuna, shugabannin ofisoshin ƙananan hukumomi da sauran jami’ai masu ruwa da tsaki a faɗin jihar da su tabbatar ba a sake amincewa ko ɗaukar waɗannan mutane a matsayin wakilan NSCDC ba.










