• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Wasu kasashen Europe uku sun amince da kasar Palastinu

aksam by aksam
May 28, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kai-tsaye: Sifaniya, Ireland da Norway sun amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance

Bayan kwashe fiye da watanni shida na kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 36,050 — cikinsu har da jarirai da yara da mata —sannan ta jikkata sama da mutum 81,026, kana.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Yanzu haka kasashen Sifaniya da Norway da Ireland a hukumance sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda suka yi watsi da Isra’ila wadda ta yi Allah wadai da matakin.

Ƙasashen uku na Turai na ganin cewa wannan matakin na su na da tasiri matuƙa kuma zai jawo wasu ƙasashen su amince da Falasɗinun a matsayin ƙasa.

A daidai lokacin da Norway ta amince da ƙasar, Ministan Harkokin Waje Espen Barth Eide ya jinjina dangane da wannan matakin.

Isra’ila ta sake tayar da bam a Rafah da ke kudancin Gaza duk da ƙasashen duniya sun nuna ɓacin ransu dangane da wani hari da Isra’ilar ta kai da ya ƙona tantuna a sansanin gudun hijira na birnin inda har mutum 45 suka rasu.

Harin wanda likitocin Gaza suka bayyana cewa ya jikkata fararen hula da dama, ya jawo Allah wadai daga ƙasashen duniya da shugabannin duniya, inda aka yi niyyar tattaunawa kan lamarin a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Irin mummunan kisan da aka yi, ƙonannun gawawwakin yara da mata da aka kai su Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya jawo Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Gutteres ya sanar da cewa “babu wani amintaccen wuri a Gaza. Akwai buƙatar a dakatar da wannan abin tsoron.”

Sifaniya, Ireland da Norway za su amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance a yau duk kuwa da fushn da Isra’ila take yi, inda aka mayar da ita saniyar-ware sakamakon luguden wuta da ta kwashe watanni bakwai tana yi a Gaza.

Ƙasashe 144 cikin 193 mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince da Ƙasar Falasɗinu, cikinsu har da Turkiyya, Rasha, China da India.

Mahukunta a biranen Madrid, Dublin da Oslo sun ce sun ɗauki matakin amince da Ƙasar Falasɗinu ne a wani yunƙuri na gaggauta hana Isra’ila ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

Duk da yake matakin da ƙasashen za su ɗauka na je-ka-na-yi-ka ne, ammasuna fata hakan zai sa sauran ƙasashen Turai su bi sahunsu.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudanar da taron gaggawa bayan wani hari da gangan da Isra’ila ta kai sansanin Falasɗinawa ‘yan gudun hijira a birni Rafah da ke kudancin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 45 kana ya jikkata fiye da mutum 250.

Wasu daga cikin mutanen an kashe su ne ta hanya yin gunduwa-gunduwa da su, yayin da aka ƙona wasu.

Ƙasar Aljeriya ce ta buƙaci a yi taron gaggawar, ko da yake ita wakiliyar dindindin ba ce ta majalisar.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Majalisar ministocin Burkina Faso ta tsawaita waadin mulkin Soji a kasar

Next Post

Bincike ya gano adadin mutanen da suka mutu a mulkin Tinibu sun…..

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Invitation !!!

Invitation !!!

August 23, 2025

Wani gwamna yayi tanadin wutar lantarki na wata guda babu daukewa ga yan jihar sa

March 5, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media