Daga Hassan Umar Gwammaja
Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Ma’aikatar Lafiya, ta kammala shirin wayar da kai da kuma bayar da ayyukan kiwon lafiyar hakora kyauta na shekarar 2025, inda fiye da mutane 6,000 daga kananan hukumomi 44 na jihar suka samu wannan hidima. An fara gudanar da wannan shiri ne a ranar 16 ga watan Agusta, kuma an kammala shi yau 22 ga watan na Agusta, a cibiyar kiwon lafiya ta farko ta Filin Mushe da ke cikin karamar hukumar Gwale.
Yayin da ya kalli yadda ake gudanar da aikin, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, wanda Sakatare Din-din-din na Ma’aikatar, Pharmacist Aminu Bashir, ya wakilta, ya yaba da jajircewar ma’aikatan lafiya da dukkan masu ruwa da tsaki da suka ba da gudunmawa wajen cimma nasarar shirin. Ya bayyana cewa wannan aiki wani ɓangare ne na dabarun gwamnatin yanzu wajen inganta damar samun ingantaccen kiwon lafiya, musamman a fannin rigakafi da kiwon lafiyar farko.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar, Pharmacist Bashir ya bayyana cewa lafiyar hakora kan kasance an raina ta, duk da cewa tana da matuƙar muhimmanci ga jin daɗin rayuwar ɗan adam. Ya jaddada cewa rashin kula da cututtukan hakora kan iya jawo matsalolin lafiya masu tsanani, inda ya nanata cewa gwamnati za ta ci gaba da saka jari a irin waɗannan shirye-shirye domin kare lafiyar jama’a.
Sakatare Din-din-din ɗin ya kuma bayyana cewa wannan shiri ya haɗa da duba hakora kyauta, bayar da magani, wayar da kan jama’a da kuma raba kayan tsaftar baki ga mahalarta. Ya ce waɗannan matakai na nufin ƙarfafa al’umma wajen ɗaukar matakan rigakafi da kuma rage yawan cututtukan hakora a cikin jama’a.
Ɗaya daga cikin masu cin gajiyar shirin, Malam Idris Garba Amin, wanda aka yi wa magani a lokacin, ya bayyana godiyarsa ƙwarai ga Gwamnatin Jihar Kano. Ya ce wannan shiri ya zo a kan lokaci, musamman ga talakawa da ba su da ƙarfin biyan kuɗin kula da lafiyar hakora. Ya yi addu’a ga nasarar wannan gwamnati tare da kiran a ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai.
Ma’aikatar Lafiya ta tabbatar da aniyar ta na ci gaba da kusantar da hidimomin lafiya ga jama’a, daidai da hangen nesan Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda kullum yake bai wa bangaren lafiya muhimmanci a matsayin ginshiƙi na mulkinsa. Jami’ai sun tabbatar da cewa za a sake gudanar da ƙarin shirye-shiryen irin wannan a nan gaba, musamman a wasu muhimman fannoni na lafiya, domin rage yawan cututtuka da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Wannan shirin wayar da kan jama’a kan lafiyar hakora kyauta ya kara nuna yadda gwamnatin jihar ke da niyyar yin aiki tare da kwararrun likitoci, abokan hulɗa da al’umma domin tabbatar da cewa babu wani ɗan jihar da aka bari a baya wajen samun muhimman hidimomin kiwon lafiya.












