• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Baya ga barazanar tafiya yajin aiki ASUU ta ambaci wasu manyan abubuwa tara

aksam by aksam
May 15, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta ba gwamnatin shugaba Bola Tinubu wa’adin makonni biyu domin biya mata bukatun ta ko ta tsunduma yajin aiki.

A jiya Talata ne shugaba kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana wa manema labarai matakin da suka dauka.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban yana cewa sun ba gwamantin Bola Tinubu wadataccen lokaci da za ta magance matsalolinsu amma ta gagara taɓuka komai.

Har ila yau shugaban kungiyar ya ce majalisar zartarwar kungiyar za ta zauna domin kara kallon lamarin.

A cewarsa majalisar zartarwar ta lura da cewa gwamnatin ta nuna halin ko in kula kan matsalolin kungiyar saboda haka dole su dauki mataki, rahoton Business Day.

Manyan bukatun kungiyar ASUU guda 9

1. Farkon abin da ASUU ta zargi gwamnatin Tinubu da shi shine rashin bada kofa domin cigaba da tattaunawa kan yarjejeniyar da suka yi da gwamnati a 2009 (2009 FGN/ASUU Agreement).

Yarjejeniyar za ta bada dama wurin samun walwala ne ga malaman jami’a domin yin aiki cikin tsari.

2. Abu na biyu shine rusa tsarin majalisun gudanar da jami’o’i da shugaba Tinubu ya yi a watan Yunin 2023.

Kungiyar ta ce rusa majalisun ya saɓa dokar kasa kuma ya haifar da giɓi babba a aikin jami’a a Najeriya.

3. Abu na gaba da kungiyar ASUU ta zargi gwamnatin a kai shine cigaba da biyan malaman jami’a albashi ta manhajar IPPIS.

Duk da cewa Bola Tinubu ya ce an cire malaman jami’o’i a tsarin tun watan Disambar bara amma kungiyar ta ce babu abin da ya canja.

4. Lamarin na hudu da zai iya jefa kungiyar yajin aiki shine fitar da sabon tsarin karatun jami’a a Najeriya.

Kungiyar ta yi watsi da sabon tsarin da gwamnati ta fitar na karatun jami’a duk da cewa gwamnatin na kokarin tilasta aiki da shi.

5. Yawaitar jami’o’in gwamnati a Najeriya shine abu na biyar da kungiyar ta koka ga gwamnatin Bola Tinubu.

Kungiyar ta ce maimakon inganta jami’o’in da ake dasu gwamantin ta dukufa wurin samar da sababbin jami’o’in da ba za ta iya daukan nauyinsu yadda ya kamata ba.

6. Abu na shida da ake dambarwa a kai shine cigaba da ɗaukan dawainiyar jami’o’i yadda ya kamata.

Kungiyar ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin karkatar da kudaden da hukumar TETFund ke amfani da su wajen raya jami’o’i zuwa harkokin lamunin dalibai.

7. Korar ma’aikatan jami’a ba bisa ka’ida ba shine abu na bakwai da kungiyar ASUU ta ke kalubalantar gwamantin Tinubu.

Kungiyar ta ce tana da rahotanni a kan yadda ake wulakanta jami’anta a jami’ar Lagos da jami’ar Kogi da jami’ar fasaha da ke Owerri.

8. Abu na takwas da kungiyar ASUU ta koka shine yadda gwamnatin to tsohe kunnuwa kan alawus da ya kamata ta biya ta.

Gwamnatin ta gaza saka kudin alawus din da kungiyar ke binta a cikin kasafin kudin shekarar 2023.

9. A karshe kungiyar ta koka kan yadda lamura suka tabarbare a Najeriya da yadda talakawa ke kara shiga kuncin rayuwa.

A cewar kungiyar, dole gwamantin Bola Tinubu ta nemo mafita domin saukaka rayuwar al’ummar Najeriya.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf; Ya Bada Goron Sallah Ga Mahajjatan Kano

Next Post

An sami karin wadanda suka rasa rayukansu a harin masallacin k/h Gezawa

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Transformación Digital y Gestión de Datos en España: La Revolución de las Plataformas de Inteligencia

April 21, 2025
Shugaban kasuwar Singa ya magantu gameda yanayin kasuwar

Shugaban kasuwar Singa ya magantu gameda yanayin kasuwar

February 7, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media