DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
An fara samun layuka a gidajen mai a fadin kasar nan abinda ya haifar da fargaba kan yiwuwar samun karancin man.
Hakan na zuwa ne a yayin da kamfanin mai na kasa NNPC ke rike da bashin Dala Biliyan 6 na kamfanunuwan kasashen waje dake shigo da tattatcen mai inda kamfanuwan suka ce NNPC na jan kafa wajen biyan kudin.
Kamfanin dillancin labarai na Reauters ya rawaito cewa kamfanin na NNPC na fama da matsalar bashi wacce ta hada da biyan kudi ga kamfanunuwan shigo da tataccen mai da ya kai Dala biliyan 5 a watan Janairu kadai.
Lamarin dai ya nuna cewa Najeriya ta dawo da bada tallafin mai da ta ayyana cirewa a watan Mayu na 2023.
Rahotanni dai sun bayyana cewa an fara samun layuka a gidajen mai dake fadin kasar nan yayin da wasu gidajen man ke a rufe.












