Daga cikin makaman da za a iya harbawa su keta ƙarƙashin ƙasa har su iso wurin da rumbunan ajiyar sinadaran nukiliyar Iran suke, daya ne kawai ba a yi amfani da shi ba zuwa yanzu, kuma Isra’ila ba ta da shi a yanzu.
Makamin shi ne GBU-57A/B – wanda ya kasance bom marar nukiliya mafi ƙarfi a duniya – da zai iya lalata rumbunan ajiyar sinadaran ƙera makamin nukiliya, kuma Amurka ce kadai ta mallake shi a duniya.
Wannan tsararren makami mai nauyin kilogiram 13,600 zai iya ketawa ƙarƙashin ƙasa domin wargaza rumbunan sinadaran ƙera nukiliyar Iran da ke binne can ƙarƙashin duwatsu.
Zuwa yanzu Amurka ba ta bai wa Isra’ila makamain ba.
Gwamnatin Amurka ta ce bom ɗin GBU-57A/B wani ”babban makami ne mai ƙarfin da zai iya ketawa ƙarƙashin ƙasa ya y tafiya mai nisa domin wargaza rumbunan da hanyaoyin da aka gina can ƙarƙashin ƙas.
Makamin mai tsawon mita shida, an yi amanna cewa zai iya tafiyar ƙafa 200 (mita 61) a cikin ƙasa kafin ya fashe. Za kuma a iya jefa wasu boma-boman su bi shi yayin da za su iya nutsewa fiye da inda ya tsaya.
Bom ɗin na MOP – da kamfanin Boeing ta ƙera shi – ba a taɓa amfani da shi ba a tarihi, to amma an taɓa yin gwajinsa a cibiyar gwajin makaman Amurka ta ‘White Sands Missile Range’ da ke jihar New Mexico.
Bom ɗin MOP ya zarta na MOAB, mai nauyin kilogiram 9,800, da ake yi wa laƙabi da ”uwar boma-bomai”, wanda aka yi amfani da shi a yaƙin Afghanistan.
”Daga nan ne rundunar sojin Amurka ta ƙudiri aniyar ƙera wasu takwarorinsa masu irin girmansa, ko ma waɗanda za su zarta shi ɓarna. Lamarin da ya sa suka samar da GBU-57A/B mai keta ƙarƙashin ƙasa,” a cewar Farfesa Paul Rogers, na cibiyar nazarin zaman lafiya a Jami’ar Bradford da ke Birtaniya UK.
Haka kuma kawo yanzu jirgin Amurka mai suna US B-2 Spirit – da ake yi wa lakabi da sha kundum – ne kawai zai iya ɗauka tare da harba bom ɗin na MOP.
Kamfanin ƙera makamai na Northrop Grumman ne ya ƙera jirgin kuma ya kasance ɗaya daga cikin jiragen yaƙin Amurka na zamani.
Kamfanin da ya ƙera jirgin ya ce, B-2 zai iya ɗaukar nauyin da ya kai kilogiram 18,000.
Rundunar sojin saman Amurka ta ce ta yi nasarar yin gwajin jirgin ɗauke da bama-boman GBU-57A/B har guda biyu, wadanda nauyinsu ya kai kilogiram 27,200.
Wannan jirgi zai iya yin tafiyar kilomita 11,000 ba tare da buƙatar sake shan mai ba, kuma zai iya tafiyar kilomita 18,500 da shan mai ɗaya, lamarin da zai ba shi damar isa kowane wur a duniya cikin sa’o’i, a cewar kamfanin da ya ƙera jirgin.
Farfesa Rogers ya ce idan za a harba bom din MOP kan ƙasa da ke da ƙarfin tsaron sararin samaniyarta, kamar Iran, jirgin B-2 zai saje ne cikin wasu jiragen yaƙin domin ɓad da kama.
Alal misali za a iya amfani da jirgin F-22 domin gigita tsaron maƙiya, sannan kuma da jirage marasa matuƙa domin gano irin ɓarnar da aka yi, don gano ko akwai buƙatar ƙarin hare-hae domin ruguza cibiyoyin tsaron samaniyar.
Farfesan ya yi ƙiyasin cewa Amurka bata da wadatattun irin waɗannan boma-boman.
“Wataƙila irinsa da suke da shi bai wuce 10 zuwa 20 ba,” in ji shi.









