Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin leken asirin soja na Isra’ila da ke kudancin ƙasar a safiyar Alhamis, ba asibiti ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka rawaito.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnati a Iran, IRNA, ne ya bayyana hakan.
IRNA ta ce harin ya nufi hedikwatar rundunar sadarwa da ba da bayanai (C4I) ta sojojin Isra’ila da wata cibiyar leƙen asiri. Ta ƙara da cewa asibitin da aka ambata abin ya shafe shi ne sakamakon girgizar fashewar bam ɗin.
Wasu kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa wani makamin Iran ya faɗa Asibitin Soroka da ke garin Beersheba a kudancin Isra’ila, inda hukumomi suka ce an samu “mummunar barna.”
Jaridun Isra’ila sun fitar da bidiyon da ke nuna tagogi sun fashe da hayaƙi mai duhu yana tashi.
Har yanzu ba a tantance adadin waɗanda suka ji rauni ba.
A halin da ake ciki, Isra’ila ta kai hari kan matatar ruwa mai nauyi ta Arak da ke Iran, inji gidan talabijin na gwamnatin Iran, inda ta ce an kwashe ma’aikata kafin harin kuma babu haɗarin zubewar wani sinadari.
Isra’ila ta riga ta yi gargaɗi cewa za ta iya kai hari kan wannan cibiyar.










