An samu matsalolin fasaha a daukar ma’aikatan na shekarar 2025, inda shafin ya rika katsewa, dalilin hakan ya sa aka dakatar da shi na wani lokaci.
An fara shirya fara wannan daukar aiki tun ranar 26 ga Yuni, amma daga baya aka dage zuwa 14 ga Yuli, sannan aka sake daga shi zuwa 21 ga Yuli.
Saboda haka, lokacin da aka tsara rufe shafin shi ne ranar 4 ga Agusta, 2025,amma sai aka kara mako guda zuwa Litinin, 11 ga Agusta.
Duk da wadannan matsaloli, alkaluman da ke shafin CDCFIB sun nuna cewa mutane 1,911,141 ne suka nemi aikin kafin rufe shafin.
A cewar alkaluman, jihohin da suka fi yawan masu nema sun hada da Kogi (116,162), Kaduna (114,536), da Benue (110,565), yayin da Bayelsa (11,669) da Lagos (14,216) suka fi karanci.
Jihohi biyar da suka fi yawan masu nema su ne Kogi, Kaduna, Benue, Kano, da Niger, wadanda suka samar da jimillar masu nema 510,174.
A bangaren wadanda suka fi karanci kuwa, Bayelsa (11,669), Lagos (14,216), Rivers (22,210), Ebonyi (23,601), da Delta (27,962) sun hada gaba daya da masu nema 99,658.
A halin yanzu, CDCFIB ta bayyana matakan da masu nema za su bi bayan kammala neman aiki na shekarar 2025 ga hukumar tsaro ta paramilitary.
A cikin wasu sakonni da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, hukumar ta gode wa masu nema tare da bayyana cewa za a tuntubi wadanda aka zaba cikin ’yan kwanaki masu zuwa, tare da umarni kan mataki na gaba.
Hukumar ta shawarci masu nema da su rika duba sakonnin imel da na waya akai-akai, tare da shiga shafin CDCFIB da kafafen sada zumunta don samun sabbin bayanai.
Ta ce: “An rufe shafin neman aiki ! An rufe shafin neman aiki na Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board. Muna gode wa duk masu nema bisa sha’awar su da jajircewa wajen yi wa kasa hidima cikin kima, gaskiya, da alfahari.
“Mataki na gaba! Za a tuntubi wadanda aka zaba cikin ’yan kwanaki masu zuwa tare da karin bayani. Don Allah ku rika duba imel da sakonnin waya, kuma ku kasance kuna binciken shafin da kuma kafafen sada zumunta don samun muhimman bayanai.”












