Wasu gungun ƴan bindiga sun sake kai kazamin hari garin Tsafe, hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, ƴan bindiga sun kashe jami’an rundunar ƴan sa-kai (CPG) tare da ƙone motoci biyu na rundunar sojin Najeriya.
Wani mazaunin garin, Malam Usman Tsafe, ya shaidawa ƴan jarida ta wayar tarho cewa ƴan bindigar sun kewaye garin ɗauke da muggan makamai.
A cewarsa, da farko ƴan bindigar sun raba kansu zuwa gida uku, inda tawagar farko ta yi yunkurin kai farmaki kwalejin horar da malaman lafiya da fasaha da ke garin.
Sauran kaso biyun kuma suka kutsa kai cikin garin, sannan suka buɗe wuta domin su tsorata jama’a kuma su samu saukin sace mutane da ɗaliban makaranta.
Jami’an tsaro sun fafata da maharan Ya ƙara da cewa ɗaukin da jami’an tsaro suka kawo a kan loƙaci, shi ne ya sa maharan suka ja da baya, suka arce zuwa cikin jeji bayan musayar wuta.
“Yayin murayar wuta da ƴan ta’addan, jami’an rundunar CPG biyu suka rasa rayuwarsu yayin ƴan bindiga suka ƙone motocin sintiri biyu na sojojin Najeriya da CPG ta Zamfara,” in ji shi.












