• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Dalilin ɗauke Sheikh Abduljabbar Daga kurkukun Kurmawa

aksam by aksam
October 14, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
479
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Yadda India wa ke sa rai da jawabin FM Modi a ranar ruwa ta India

Ghana Na Shirin Kakkaɓe Yaduwar Makamai Marasa Lasisi

China ta sauya tsarin cinikayyar ta da duniya ba tare da Dalar Amurka ba

<span;>Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta na bayyana cewa an dauke fitaccen malamin addinin Musulunci Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, daga gidan yarin Kurmawa da ke Kano zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
<span;>‎
<span;>‎Wata majiyar kusa da iyalan malamin ta shaida wa AKSAMMEDIA cewa, daga baya suka ji rade-radin cewa an kai shi gidan yarin Kuje da ke Abuja, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mabiyansa da ‘yan uwa.
<span;>‎
<span;>‎A wata sanarwa da Askia Nasiru Kabara ya fitar a madadin iyalan Shaikh Abduljabbar, ya ce suna zargin akwai manufar siyasa ko wata bakar manufa a bayan daukar malamin daga Kurmawa zuwa wani wuri daban, musamman a wannan lokaci da ake samun sabbin jita-jita kan batun da ya shafi Shaikh ɗin.
<span;>‎
<span;>‎“Mun sani hukumar kula da gidajen yari ta kasa tana da ikon mayar da fursuna duk inda ta ga dama, amma abin mamaki shi ne me ya sa sai yanzu aka dauke shi bayan shekaru hudu da yake a Kurmawa?” in ji Askia.
<span;>‎
<span;>‎Ya kara da cewa, tun bayan barkewar maganar Lawan Triumph, an fara yada jita-jitar cewa za a saki Shaikh Abduljabbar, wanda hakan ya jawo cece-kuce daga bangaren kungiyar Izala.
<span;>‎
<span;>‎Iyalan Shaikh din sun bayyana damuwarsu cewa yanzu da aka ce an mayar da shi Abuja, ba su da tabbacin yadda ake kula da shi, musamman wajen abinci da lafiya, domin kafin yanzu suna kai masa abinci daga gida.
<span;>‎
<span;>‎A karshe, iyalan sun bukaci  Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sauran Manyan mukarraban gwamnatinsa da su saka ido a kan lamarin
<span;>‎
<span;>‎Kazalika sun bukaci Gwamnatin jihar Kano  da kungiyoyin kare hakkin dan adam saka ido  Domin kare hakkin sa da yin abin da ya dace.
<span;>‎
<span;>‎“Abin da ya faru da Shaikh Abduljabbar ya zama abin damuwa da ya shafi tsaro da adalci a kasa baki daya. Bai kamata wasu kalilan su yi wasa da rayuwar mutum ba,” in ji sanarwar.
<span;>‎
<span;>‎Iyalan sun roki gwamnati da hukumomin tsaro da su binciki lamarin da gaggawa domin tabbatar da cewa ba a tauye masa hakkinsa ba.

Share192Tweet120SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnatin tarayya zata rage bashin da zata ciyo da Tiriliyon hudu na fannin lantarki

Next Post

Zuwa gaba Matatar Dangote ce zata zama makomar Najeriya: hasashen Masana

aksam

aksam

RelatedPosts

Yadda India wa ke sa rai da jawabin FM Modi a ranar ruwa ta India
Uncategorized

Yadda India wa ke sa rai da jawabin FM Modi a ranar ruwa ta India

by aksam
October 28, 2025
Ghana Na Shirin Kakkaɓe Yaduwar Makamai Marasa Lasisi
Uncategorized

Ghana Na Shirin Kakkaɓe Yaduwar Makamai Marasa Lasisi

by aksam
October 27, 2025
China ta sauya tsarin cinikayyar ta da duniya ba tare da Dalar Amurka ba
Uncategorized

China ta sauya tsarin cinikayyar ta da duniya ba tare da Dalar Amurka ba

by aksam
October 26, 2025
China ta ƙara wa Pakistan ƙarfi a fannin fasahar da take Amfani da Ita
Uncategorized

China ta ƙara wa Pakistan ƙarfi a fannin fasahar da take Amfani da Ita

by aksam
October 25, 2025

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kwamishinan  ‘Yan Sandan Kano CP M.U.Gumel Ya Gana Da Shugabannin Kafafen Yada Labarai, A Jajiberan Fara Sauraren Shari’ar Gwamnan Jihar A Kotun Koli

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano CP M.U.Gumel Ya Gana Da Shugabannin Kafafen Yada Labarai, A Jajiberan Fara Sauraren Shari’ar Gwamnan Jihar A Kotun Koli

December 20, 2023
Yau Ce Ranar Radiyo Ta Duniya:- Ko Wace Godinmawa Radiyo Take  Baku A Cikin Al’amuran Rayuwarku ?

Yau Ce Ranar Radiyo Ta Duniya:- Ko Wace Godinmawa Radiyo Take Baku A Cikin Al’amuran Rayuwarku ?

February 13, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Muna goyon bayan hukumar KAROTA akan yaki da kasa kaya a kan titi: Kungiyar Yan tebura ta IBB

Muna goyon bayan hukumar KAROTA akan yaki da kasa kaya a kan titi: Kungiyar Yan tebura ta IBB

March 11, 2025
Rashin tsaro da tsadar takin zamani ya haifar da durkushewar harkokin kasuwanci

Rashin tsaro da tsadar takin zamani ya haifar da durkushewar harkokin kasuwanci

October 30, 2025
Yadda Sarki Aminu Da ‘Yan Sanda Suka Kwace Ni A Hannu Wasu Matasa:– Dan Majalisar NNPP

Yadda Sarki Aminu Da ‘Yan Sanda Suka Kwace Ni A Hannu Wasu Matasa:– Dan Majalisar NNPP

July 22, 2024
Yadda kungiyar mata sufaye suka jagoranci gudanar da addu’a kan halin da al’umma ke ciki

Yadda kungiyar mata sufaye suka jagoranci gudanar da addu’a kan halin da al’umma ke ciki

July 27, 2024
An  Bude Sabuwar Kasuwar Sayar Da:-  Hatsi, Dabbobi, Da Suran Kayayyakin  Masarufi  A Garin Dutse Dake Kantitin Kaduna Zuwa Abuja A Yakin Karamar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna

An Bude Sabuwar Kasuwar Sayar Da:- Hatsi, Dabbobi, Da Suran Kayayyakin Masarufi A Garin Dutse Dake Kantitin Kaduna Zuwa Abuja A Yakin Karamar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna

February 6, 2025

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media