• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Dalilin ɗauke Sheikh Abduljabbar Daga kurkukun Kurmawa

aksam by aksam
October 14, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
480
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

<span;>Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta na bayyana cewa an dauke fitaccen malamin addinin Musulunci Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, daga gidan yarin Kurmawa da ke Kano zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
<span;>‎
<span;>‎Wata majiyar kusa da iyalan malamin ta shaida wa AKSAMMEDIA cewa, daga baya suka ji rade-radin cewa an kai shi gidan yarin Kuje da ke Abuja, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mabiyansa da ‘yan uwa.
<span;>‎
<span;>‎A wata sanarwa da Askia Nasiru Kabara ya fitar a madadin iyalan Shaikh Abduljabbar, ya ce suna zargin akwai manufar siyasa ko wata bakar manufa a bayan daukar malamin daga Kurmawa zuwa wani wuri daban, musamman a wannan lokaci da ake samun sabbin jita-jita kan batun da ya shafi Shaikh ɗin.
<span;>‎
<span;>‎“Mun sani hukumar kula da gidajen yari ta kasa tana da ikon mayar da fursuna duk inda ta ga dama, amma abin mamaki shi ne me ya sa sai yanzu aka dauke shi bayan shekaru hudu da yake a Kurmawa?” in ji Askia.
<span;>‎
<span;>‎Ya kara da cewa, tun bayan barkewar maganar Lawan Triumph, an fara yada jita-jitar cewa za a saki Shaikh Abduljabbar, wanda hakan ya jawo cece-kuce daga bangaren kungiyar Izala.
<span;>‎
<span;>‎Iyalan Shaikh din sun bayyana damuwarsu cewa yanzu da aka ce an mayar da shi Abuja, ba su da tabbacin yadda ake kula da shi, musamman wajen abinci da lafiya, domin kafin yanzu suna kai masa abinci daga gida.
<span;>‎
<span;>‎A karshe, iyalan sun bukaci  Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sauran Manyan mukarraban gwamnatinsa da su saka ido a kan lamarin
<span;>‎
<span;>‎Kazalika sun bukaci Gwamnatin jihar Kano  da kungiyoyin kare hakkin dan adam saka ido  Domin kare hakkin sa da yin abin da ya dace.
<span;>‎
<span;>‎“Abin da ya faru da Shaikh Abduljabbar ya zama abin damuwa da ya shafi tsaro da adalci a kasa baki daya. Bai kamata wasu kalilan su yi wasa da rayuwar mutum ba,” in ji sanarwar.
<span;>‎
<span;>‎Iyalan sun roki gwamnati da hukumomin tsaro da su binciki lamarin da gaggawa domin tabbatar da cewa ba a tauye masa hakkinsa ba.

Share192Tweet120SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Gwamnatin tarayya zata rage bashin da zata ciyo da Tiriliyon hudu na fannin lantarki

Next Post

Zuwa gaba Matatar Dangote ce zata zama makomar Najeriya: hasashen Masana

aksam

aksam

RelatedPosts

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo
Uncategorized

Halifatul Akabar Sheikh Ahmad Abdullah Mai Kano Jallo Ya Halarci Mulundin Garin Zangon Nkawkawo

by aksam
September 5, 2026
Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi  Annabi Muhammadu SWA  A Garin Nkawkawo
Uncategorized

Irin Yadda Aka Gudanar Da Zagayen Mauludn Tunawa Ga Ranar Da Aka Haifi Annabi Muhammadu SWA A Garin Nkawkawo

by aksam
September 1, 2026
Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka
Uncategorized

Kasar Ghana Ta Bayyana Shirinta Na ƙara Samar Da Wutar Lantarki Domin Sayarwa Najeriya Da Sauran ƙasashen Yammacin Afirka

by aksam
August 26, 2026
Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano
Uncategorized

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Dakile Wata Gobara A Rano

by aksam
August 26, 2026

Comments 0

  1. Hussain Kabir minjibir says:
    11 months ago

    Headlines din ku yana saɓawa da labarin ku , saboda haka idan akwai yaudara za’a dinga kaucewa labaran ku

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai

NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai

April 26, 2026
Yan Bindiga Sun Sace Basarake A Katsina

Wasu Ƴan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Janar Mai Ritaya Da Matarsa A Katsina

May 31, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media