• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Sarki Aminu Da ‘Yan Sanda Suka Kwace Ni A Hannu Wasu Matasa:– Dan Majalisar NNPP

aksam by aksam
July 22, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home TSARO
ADVERTISEMENT
475
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Wasu gungun matasa sun yi wa dan majalisar dokokin jihar Kano Abdul-Majid Umar dukan tsiya a wani taron da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero ya halarta a ranar Asabar.

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

Umar dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwale, wasu Matasa ‘yan mazabarsa ne suka kai masa hari a unguwar Goron Dutse.

Dan majalisar a ranar Litinin din nan ya ce sarki Aminu Ado Bayero da ‘yan sanda sune suka kwace shi daga hannun matasan.

Idan za a iya tunawa Aksam Media ta rawaito Aminu Ado-Bayero, a ranar Asabar din da ta gabata, ya halarci taron addu’o’i na shekara-shekara da ake yiwa kasa da kano domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali , wanda shugabannin darikar Tijjaniyya suka shirya a gidan Marigayi Sheikh Isyaku Rabiu da ke Goron Dutse, a karamar hukumar Gwale ta Jihar

Umar wanda ya zauna a gefen sarkin a wajen taron, amma matasan sun far masa ne jim kadan da barin wurin taron.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, matasan sun zarge shi ne da goyon bayan kudirin tsige sarkin.

Rahotanni sun ce matasan sun raunata dan majalisar ne kafin ya tsere cikin motar ‘yan sanda da ke wajen taron.

Dan majalisar ya shaida wa sashen Hausa na BBC a ranar Litinin cewa, dubban magoya bayan sarkin ne suka kai masa hari bayan ya bar taron ba tare da sanin ya kamata ba.

Umar ya ce ya bar wurin ne a lokacin da ya lura da cewa wurin babu tsaro.

“Bayan da hambararren sarkin ya isa wurin taron, sai magoya bayansa suka fara zagina da abokan aikina, suna zargin mu da soke dokar majalisar masarautun 2019 da ta kai ga tsige Sarkin.

“Sarkin da aka tube ya tare wani daga cikin fadawansa da ya yi yunkurin buge ni. Sarkin da kansa ya yi amfani da hannunsa wajen tare dukan da bafaden ya kawo, ya kuma yi wa wani wanda ya sake yunkurin duka na tsawa,” in ji Mista Umar.

Umar ya ce ya yanke shawarar barin taron ne lokacin da ya lura cewa shi kadai ne jami’in gwamnati a wajen taron.

“Na kara shiga damuwa bayan na bar wurin taron yayin da mutane dauke da muggan makamai suka far min. Na yi sauri na shiga motar ‘yan sanda. Da haka aka kubutar da ni daga harin.

“Magoya bayana biyu sun jikkata lokacin da muke kokarin barin wurin taron”, in ji dan majalisar.

Sai dai daya daga cikin hadiman sarkin kan harkokin kafafen yada labarai, Khalid Uba Adamu ya musanta cewa matasan suna cikin tawagar sarkin.

Ya ce Sarki Aminu Ado Bayero ya isa wurin taron ne da dimbin magoya bayansa, amma babu daya daga cikinsu da ke dauke da makami.

Rikicin masarautar Kano ya fara ne bayan da ‘yan majalisar a ranar 23 ga Mayu, 2024 suka soke dokar majalisar masarautun jihar ta 2019, wadda tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu hudu.

Share190Tweet119SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Dangote ya shirya sayar da matatar man fetur dinsa kan wani babban Dalili

Next Post

Shugabancin tashar Yankaba ya dauki matakin dakile yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tashar

aksam

aksam

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

by Khadija Maitaya
July 24, 2026
Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa
LABARAI

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

by Khadija Maitaya
July 10, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

by Khadija Maitaya
June 22, 2026
Rundunar  Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, Godwin Emefiele;  Zai Yi Bukukuwan Kirsimeti Dana Sabuwar Shekara A Gidan Gyaran Hali

Mai Bincike Akan Bankin CBN Ya Bankado Asusun 593 Na Kasashen Ketare Masu Alaka Da Emefiele

December 22, 2023
Yadda kungiyoyin Musulmai suka yi gangamin addu’ar neman nasara ga kasar palatine

Yadda kungiyoyin Musulmai suka yi gangamin addu’ar neman nasara ga kasar palatine

November 3, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media