Alhaji Aliko Dangote ya fara shirin siyar da matatar man fetur ɗinsa wacce aka kwashe shekaru ana ginawa a jihar Legas
Attajirin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika ya ce a shirye yake ya siyar da matatar man fetur ɗin ga kamfanin NNPCL
Ya nuna cewa wasu mutane ba su ji daɗin yadda ya shigo cikin harkar man fetur ba shiyasa suke ƙoƙarin zame masa ƙarfen kafa
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana hakan ne dai yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Premium Times a ranar Lahadi.
Hakan na zuwa ne bayan Dangote ya ƙalubalanci hukumar NMDPRA kan batun cewa man dizal da yake samarwa bai kai ingancin wanda ake shigo da shi daga ƙasar waje ba.
Attajirin ya yi magana ne a yayin da dangantaka ta fara yin tsami tsakaninsa da hukumomi a ɓangaren makamashi na Najeriya.
“Su (NNPCL) su zo su siya sannan su ci gaba da gudanar matatar man fetur ɗin yadda za su iya.
Sun kira ni da mai yin kaka gida. Wannan zargin kuskure ne, amma ba komai. Aƙalla idan suka siya zan kauce na ba su waje.”












