Hedikwatar tsaro ta ce ta tura dakarunta zuwa ga manoma a faɗin Jihohin Arewa musamman yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya a Najeriya domin tabbatar da ganin an magance matsalar da manoma ke fuskanta tare da magance matsalar karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki.
Daraktan yada labarai na Hedkwatar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata Sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A cewar sa an tura dakarun ne domin baiwa manoma da dama damar shiga gonakinsu.
Yayin da damina ta kankama a halin yanzu mun girke Sojoji a wasu yankunan arewaci musamman a Jihohin Arewa maso Yamma, Da Arewa ta tsakiya domin kare manoma.
“Hakan ya baiwa manoma da dama damar shiga gonakinsu don yin noma cikin kwanciyar hankali domin samun amfanin gona mai yawa,” inji shi.
Dimokuradiyya TV ta tuna cewa Sufeto Janar na ƴan Sanda Kayode Egbetokun ya kuma ce ƴan Sanda sun fara sintiri a gonaki domin kara kwarin gwiwa ga manoma.
A Arewa maso Gabas mun fara sintiri a gonaki domin baiwa manoma kwarin gwiwa su koma gona, Shugaban ƙasa ya damu matuƙa da hakan kuma muna yin iya kokarinmu.
“Amma kuma ya ƙara da cewa yanayin tsaro a Najeriya yana da sarkakiya da yanayi daban-daban.” Inji shi
Don haka a kwanakin baya Shugaban ƙungiyar manoma ta Najeriya Kabir Ibrahim ya tabbatar da cewa an samu karuwar tsaro a gonaki a duka faɗin ƙasar nan.
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ƴan ta’adda da masu aikata laifuka suka yi barna a yankunan a cikin watanni shida da suka gabata.
An bayyana cewa an kashe daruruwan manoma tare da yin garkuwa da wasu a yankin a cikin kwatar farko na shekarar 2024.
SBM wata Hukumar Fikira ta ce manoma a Arewa sun biya kimanin Naira Miliyan 139 a matsayin harajin noma ga barayin daji, da suka nemi akalla Naira Miliyan 224 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023.
Hakan ya taimaka wajen hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya.
Hauhawar farashin abinci a Najeriya ya karu daga kashi 40 zuwa kashi 87 cikin 100 bisa kididdigar da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar a watan Yuni.









