Daga Khadeeja Salisu Danmaliki
Gwamnatin Tarayya ta ce Sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro na bukatar aƙalla harsasai Miliyan 350 a duk shekara domin gudanar da ayyukansu daban-daban inda ta ƙara da cewa Gwamnati tana kashe akalla dalar Amurka 2 kan kowane alburushi guda.
Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle wanda ya bayyana hakan a Abuja a jiya Laraba ya zargi gwamnatocin da suka shude a kan abin da ya bayyana a matsayin “gazawar Gwamnati wajen samar da kayan aikin soja da na tsaro.
Matawalle ya yi magana ne jim kadan bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ma’aikatar tsaro da masana’antun ƙera makamai ta Najeriya (DICON) da hukumar kimiyyar ƙere-ƙere ta ƙasa (NASENI) kan kafa masana’antar kera makamai a Najeriya.
Mataimakin shugaba hukumar NASENI Khalil Halilu ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar wani muhimmin mataki ne na karfafa karfin tsaron ƙasar nan da kuma samun dogaro da kai wajen kera kayan aikin Soja.
Shima da yake magana Ministan Tama da karafa Shuaibu Audu ya bayyana cewa kamfanin karafa na Ajaokuta ya samar da ingantaccen matsuguni ga rukunin masana’antar kayan aikin Soji









