• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Za A Kara Kudin Alawusdin ‘Yan Bautar Ƙasa – Hukumar NYSC

aksam by aksam
September 4, 2024
Reading Time: 1 min read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

Hukumar NYSC ta tabbatarwa da ƴan yi wa ƙasa hidima cewa za a ƙara kuɗin alawus na N33,000 da ake biyan su a duk wata da zarar gwamnatin tarayya ta aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙarancin.

RelatedPosts

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

Shugaban hukumar NYSC, Yusha’u Ahmed, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya ziyarci jihohin Kebbi da Sokoto domin jawabi ga ƴan yiwa ƙasa hidima na 2024 Batch ‘B’ na biyu a sansanonin horaswa na jihohin biyu.

Ya bayyana cewa gudunmawar da ƴan yi wa ƙasa hidima ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa yana da matuƙar muhimmanci, inda ya jaddada cewa ya kamata ƴan yiwa kasa hidima su yi amfani da shekarar hidimar su wajen bunƙasa kansu da shirya wa kansu ingantacciyar makoma.

Shugaban hukumar ya ce, “Aƙalla, ku koyi sana’a yayin da kuke sansanin, kuma bayan kammala tsarin horaswa, dama bayan fita daga sansanin.

Ku yi ƙoƙarin koyon sana’ar da za ta ba ku damar ƙirƙirar ayyukan yi da ɗaukar ma’aikata maimakon neman aikin yi. Muna da tsofaffin ƴan yiwa ƙasa hidima da yawa a faɗin ƙasar da suke yin nasara a cikin sana’o’in su daban-daban a yau.”

“Hukumar NYSC ta haɗa hannu da ƙungiyoyi masu nagarta da yawa kamar Babban Bankin Najeriya (CBN), Bankin Masana’antu (BOI), Unity Bank, Access Bank, da gidauniyar NNPC da sauransu, waɗanda ke taimakawa wajen ba da rance da tallafi ga ƴan yiwa ƙasa hidima.”

Ya tabbatar musu da cewa za a tabbatar da tsaron lafiyar su a duk tsawon shekarar hidimar su.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda kungiyar mahakiratu illallah da wasu kungiyoyin tijjanawa mata suka gudanar da taron addu’a a fadar mai Martaba Sarkin kano

Next Post

gwamnatin tarayya ta magantu gameda zargin rashin jituwa tsakanin Tinubu da mataimakin sa

aksam

aksam

RelatedPosts

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa
Uncategorized

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

by aksam
June 15, 2026
Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato
Uncategorized

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

by aksam
June 2, 2026
Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa
Uncategorized

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

by aksam
May 31, 2026
Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya
Uncategorized

Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya

by aksam
May 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Ziyarci Al’ummomin Da Ambaliya Ta Yi Wa Barna A Kasarsa

August 10, 2024

Die Bedeutung von Plattformbewertungen in der modernen Online-Casino-Branche

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media