Akalla ‘yan mata da zawarawa 300 ne gwamnatin jihar Kebbi ta yi masu auren gata a ranar Lahadin da ta gabata a Birnin Kebbi
Gwamnatin jihar ta kashe naira miliyan 21 don biyan kowacce amarya naira dubu 70 kudin sadaki bayan yi masu kayan daki
Gwamnan jihar, Nasir Idris ya ce hakan zai taimaka wajen rage zawarawan da ke yawo a gari da mazan da ke son yin aure amma babu hali









