Yaƙin da ake yi a Iran ya ƙara buƙatar man fetur daga matatar Dangote ta dala biliyan 20 da ke Legas, lamarin da ya taimaka wajen ƙara arzikin attajirin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, da sama da dala biliyan 5 tun daga watan Fabrairun wannan shekara.
A cewar wani rahoto na jaridar New York Times, matatar Dangote ta zama muhimmiyar cibiyar samar da man fetur, yayin da rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya da Rasha suka tilasta wa wasu ƙasashe neman wasu hanyoyin samun makamashi.
Rahoton ya ce matatar ta Dangote ta kai cikakken ƙarfin aiki jim kaɗan kafin ƙaddamar da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Hakan ya sa matatar ta ƙara samun muhimmiyar rawa a kasuwar man fetur ta duniya, musamman a lokacin da ake fuskantar matsaloli wajen samar da makamashi daga wasu yankuna.









