Kotun Majistare Mai Daraja ta Ɗaya da ke Kafin Maiyaki, Ƙaramar Hukumar Kiru ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Chief Magistrate Muhammad Alhaji Isa, ta yanke wa wani matashi mai suna Iliyasu, ɗan asalin Fakin Ikara a Jihar Kaduna, hukuncin zaman gidan ajiya da gyaran hali na tsawon watanni uku.
An yanke masa hukuncin ne bayan an same shi da laifin satar kayan injin motar kurkura. Lamarin ya faru ne bayan mai kayan, mai suna Munkaila, ya ba Iliyasu amanar gadin kayan na tsawon kwanaki uku.
A cewar bayanin da aka gabatar a gaban kotu, a cikin dare ne wanda aka yanke wa hukuncin ya sace kayan injin ɗin motar, ya kuma saka su cikin wani babban buhu.
Bayan fitowarsa daga kotu, wakilinmu Dantala Uba Nuhu Kura ya tattauna da Munkaila, wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma matakin da ya kai ga gurfanar da matashin a gaban kotu.










